Ƙasar Sin ta mayar da martani ga yadda Nancy Pelosi ta je yankin Taiwan na ƙasar

Daga CMG HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, yadda shugabar majalisar wakilan ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta rufe kunnenta game da kin amincewar da ɓangaren ƙasar Sin ta nuna.

Inda ta tafi ziyara a yankin Taiwan na ƙasar, ya saba wa manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da bayanan haɗaɗɗun sanarwoyi guda 3 da ƙasashen Sin da Amurka suka gabatar a baya, lamarin da ya girgiza tushen alaƙar Sin da Amurka, da keta ikon ƙasar Sin na mulkin kai da na kare cikakken yankin kasa. Saboda haka ƙasar Sin ta yi Allah wadai da lamarin da babbar murya, tare da nuna matuƙar rashin jin dadi ga ɓangaren ƙasar Amurka.

A sa’i ɗaya, rundunar sojojin ƙasar Sin ta PLA ta sanar da shirin ƙaddamar da atisayen soja a wasu yankunan dake dab da yankin Taiwan na ƙasar, tsakanin ranar 4 zuwa ranar 7 ga watan nan na Agusta.

Kakakin zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin, da kwamiti mai kula da harkar hulda da ƙasashen waje na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar ƙasar, da ofishin kula da ayyuka masu alaƙa da yankin Taiwan na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, dukkansu sun bayyana takaici da kin amincewa game da tafiyar Nancy Pelosi zuwa yankin Taiwan na ƙasar Sin.

Fassarawar Bello Wang/Jamila Zhou)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *