Ƙasar Sin ta samu kyawawan sakamako a ɓangaren kiwon lafiyar al’umma

Daga CMG HAUSA

Mataimakin shugaban hukumar kula da lafiyar al’umma ta ƙasar Sin, Cao Xuetao, ya ce jarin da Sin ta zuba a ɓangaren lafiyar al’umma, ya haifar da kyawawan sakamako ba tare da lakume maƙudan kuɗi ba.

Cao Xuetao, ya bayyana haka ne yayin taron ƙoli na duniya kan lafiya da aka fara ranar Asabar, inda ya ce matsakaicin tsawon rayuwar al’ummar Sinawa ya kai shekaru 78.2, kuma manyan alkaluman auna ingancin lafiya a ƙasar sun haura matsakaicin mizanin matsakaita da manyan ƙasashe ta fannin kuɗin shiga.

Taron wanda jami’ar Tsingua ta shirya, ya samu halartar kimanin fitattun masana da mambobin hukumomin ƙasa da ƙasa kimanin 70 daga ƙasashe da yankuna 10.

Ya ƙara da cewa, Ƙasar Sin za ta ci gaba da shiga ana damawa da ita cikin ayyukan kiwon lafiya a duniya, da aiwatar da shirin raya duniya da haɗa hannu da sauran ƙasashe domin yaƙi da annobar COVID-19, yana mai cewa, ƙasar za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da musaya kan harkokin lafiya da kuma ƙoƙarin gina al’ummar duniya mai lafiya ga kowa.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha