Ƙasar Sin ta tsara matakai 20 na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar Covid-19

Daga CMG HAUSA

Zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin (JKS), ya gana a yau Alhamis, inda mambobinsa suka saurari rahoto game da matakan da ake ɗauka domin shawo kan cutar COVID-19, kana sun tattauna tare da tsara matakai 20, na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar.

Shugaban ƙasar Sin kana babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci zaman tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Taron ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun tsare-tsaren kwamitin ƙolin JKS, tare da nacewa aƙidar sanya rayuwar al’umma sama da komai, da wanzar da manufar daƙile annobar a duk inda ta ɓullar.

Kazalika, Sin za ta yi ƙoƙarin daidaita aikin kandagarkin cutar da na bunƙasa tattalin arziki da zaman al’umma, ta yadda za a kai ga kare rayukan al’umma da kiwon lafiyar su, a yayin da kuma tabbatar da rage mummunan tasirin annobar zuwa mataki mafi kankanta, ta fuskar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma.

Mai fassara: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *