Ƙasar Sin ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance fashin teku a gaɓar tekun Guinea

Daga CMG HAUSA

Zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Geng Shuang, ya yi kira ga ƙasa da ƙasa, su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen shawo kan fashin teku a yankin gaɓar tekun Guinea.

Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya, yayin zaman da Kwamitin Sulhu na MƊD ya gudanar kan gabar ta tekun Guinea.

Jakadan na ƙasar Sin, ya ce ya kamata ƙasashen duniya su taimakawa ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yammacin Afrika da takwararta ta ƙasashen tsakiyar Afrika, da hukumar kula da gaɓar tekun Guinea da sauran kungiyoyi da hukumomin shiyyoyi, wajen taka muhimmiyar rawa domin ƙarfafa ayyukan yaki da fashin teku.

Ya ce a shekarun baya-bayan nan, an gayyaci sojojin ruwa na ƙasar Sin, su gudanar da atisayen yaƙi da fashin teku da takwarorinsu na Nijeriya da Kamaru da sauran wasu ƙasashe, haka kuma an samar da kayayyakin aiki a matsayin tallafi ga ƙasashen dake gaɓar teku.

Har ila yau, cikin watan Mayun bana, sojojin ƙasar Sin sun gudanar da wani taron ƙarasa juna sani kan yanayin tsaro a yankin gaɓar tekun Guinea, inda ta cimma wata muhimmiyar yarjejeniya da ƙasashen yankin.

Bugu da ƙari, Geng Shuang, ya ce a nan gaba, ƙasar Sin za ta ci gaba da musaya da ƙasashen dake gabar teku a fannonin tsaro da ayyukan ‘yan sanda da sojoji da sauran wasu ɓangarori da faɗaɗa haɗin gwiwa a aikace da taka rawa wajen bayar da ƙarin gudunmuwa ga tsaron gabar tekun Guinea.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha