Ƙasar Sin ta yi kira da a nace kan ra’ayin haɗin gwiwa na haƙiƙa a taron G20 a Indunusiya

Daga CMG HAUSA

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya yi kira a yau Juma’a ga ƙasashen duniya a tsibirin Bali na ƙasar Indunusiya, da su tsaya tsayin daka kan haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban, da raya hulɗa mai inganci a wannan lokaci mai cike da ƙalubaloli.

Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G20 da aka gudanar a tsibirin Bali na ƙasar Indunusiya.

Wang Yi ya ce, da farko, ya kamata ƙasashe su kasance abokan hulɗa tare da mutunta juna da tuntubar juna bisa daidaito. Kamata ya yi a tafiyar da harkokin ƙasa da ƙasa ta hanyar tuntubar juna tsakanin ƙasashe, kana a kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa cikin haɗin gwiwa.

Na biyu, ya kamata ƙasashe su kasance abokan zaman tare cikin lumana da hadin gwiwar moriyar juna. Yana mai cewa, sai wata ƙasa ta mutunta tsaron wasu kuma ta kiyaye tsaron kowa ne, kafin ta iya samun nata tsaro na haƙiƙa.

Wang ya kara da cewa, yadda wata ƙasa ta fifita tsaronta a kan tsaron sauran ƙasashe da kuma ƙarfafa kawancen soji, na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙasashen duniya, da kuma sanya kanta cikin rashin kwanciyar hankali.

Kana na uku, ya kamata kasashe su kasance abokan haɗin gwiwa ba tare da wata rufa-rufa ba, da damawa da kowa, da yin cudanya da juna. Wang ya ce, ya kamata takara tsakanin kasa da kasa ta kasance mai adalci, kuma bai kamata ta zama mummunar gasa ba ko ma yin fito na fito da juna.

Fassarawar Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *