Daga CMG HAUSA
A yayin da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) ke gabatar da rahoto a lokacin buɗe taron wakilan jam’iyyar karo na 20, da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata, ya yi cikakken bayani kan halayyar musamman game da manufar aiwatar da dukkan ayyukan gwamantin Sin bisa tsarin dimokuraɗiyya, gami da fifikon manufar.
Hakan, ya nuna yadda za a aiwatar da harkokin ƙasar bisa tsarin dimokuraɗiyya na gurguzu, da yadda ƙasashe daban-daban za su fahimci ingancin tsarin dimokuraɗiyyar Sin.
Manufar aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tsarin dimokuraɗiyya ta ƙunshi ɓangarorin gudanar da zaɓe, da tattaunawa da tsai da kuɗuri game da matakan gwamnati, da kulawa da sa ido kan harkokin ƙasar, duk ƙarƙashin tsari na dimokuraɗiyya, ta yadda za a fahimci bukatun jama’a a fannonin harkokin siyasa da zaman al’umma.
Tsarin dimokuraɗiyya tsakanin ƙasashe ya sha bamban. Idan har tsari ya dace da yanayin da ƙasar ke ciki, to, zai amfani al’ummar ƙasar.
JKS za ta ci gaba da ƙoƙarin aiwatar da manufar tafiyar da dukkan ayyuka bisa tsarin dimokuraɗiyya, don tabbatar da jama’a a matsayin jigon ƙasa, gami da samar da gudunmowa ga aikin inganta tsare-tsaren siyasa dake shafar muradun bil-Adam.
Mai fassara: Bello Wang