Ƙasar Sin: Yunƙurin Amurka na yin tasiri kan ƙasashen yankin tekun Indiya da Fasifik bai dace da muradun ƙasashen ba

Daga CMG HAUSA

Dan majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya ce yunƙurin Amurka na samar da ƙarin tasiri kan ƙasashen yankin tekun Indiya da Fasifik, bai dace da muradun ƙasashen dake yankin ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa ta kafar bidiyo da Luhut Binsar Pandjatan, jami’in ƙasar Indonesia mai kula da dangantakarta da ƙasar Sin.

A cewar Wang Yi, tuni yankin gabashin Asia ke da tsarinsa na haɗin gwiwa karkashin kungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya wato (ASEAN), yana mai cewa ƙungiyar ita ce jigon tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Ya ce yunƙurin Amurka kan yankin ya saba da yanayin na zamani, kuma ba shi ne muradi na bai daya kuma mai dorewa na ƙasashen yankin ba.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *