Daga CMG HAUSA
Biyo bayan koma bayan da aka fuskanta sanadiyyar annobar COVID-19 da sauran matsaloli daga waje, babban bankin ƙasar Sin, zai inganta aiwatar da wasu manufofin kuɗi domin taimakawa dukkan ɓangarorin tattalin arziki.
Yayin taro karo na 3 na ministocin kudi na ƙasashen G20 masu ƙarfin tattalin arziki, Gwamnan babban bankin ƙasar Sin Yi Gang, ya gabatar da sabon bayani game da ci gaban tattalin arziki da harkokin kuɗi na Sin yayin taron, yana mai cewa hauhawar farashin kayayyaki na matsakaicin mataki, kuma ana sa ran matakin zai daidaita.
Ya ce bankin zai inganta samar da tsarin taimakawa manyan kamfanoni rage fitar da hayaki mai guba da inganta hadin gwiwar aiwatar da matakan tunkarar sauyin yanayi na G20, ta yadda ɓangaren hada-hadar kudi zai samu damar taimakawa manufofin kai wa matsayin koli na fitar da hayaki mai guba da kuma cimma daidaito tsakanin hayakin da abubuwan dake shawo kansa.
Taron, ƙarƙashin shugabancin Indonesia, ya gudana ne a birnin Bali, a ranekun 15 da 16 ga wata inda aka samu mahalarta a zahiri da kuma ta kafar bidiyo. Yayin taron, an kuma tattauna game da tattalin arzikin duniya da ajandar kiwon lafiya ta duniya da tsarin hada-hadar kudi na ƙasa da ƙasa da da zuba jari kan ababen more rayuwa da kuma batun haraji na duniya.