Ƙasashen Afirka na ƙara gamsuwa da shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya

Daga SAMINU HASSAN

Yayin da wasu sassan na ’yan siyasar ƙasashen yamma ke nuna shakku kan sahihancin niyyar ƙasar Sin, game da cudanyarta da ƙasashen Afirka, har ma wasu ke zargin cewa wai Sin na danawa ƙasashen na Afirka tarkon bashi, a hannu guda, masharhanta da dama na ganin wannan zargi ba shi da tushe ko makama.

Ga misali, ƙarƙashin shawarar nan ta ziri ɗaya da hanya daya, ƙasar Sin ta yi haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka da dama, wajen samar da manyan ababen more rayuwa masu matuƙar tasiri ga ci gaban ƙasashen na Afirka.

Ga misali, a baya bayan nan, masu fashin baki da dama na ci gaba da jinjinawa aikin layin dogo na SGR da ya haɗa biranen Mombasa da Nairobin ƙasar Kenya a takaice. Wannan aiki ko shakka babu, ya samar da babbar dama ta bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Kenya ta sassa da dama.

Bayan fara aiki da wannan layin dogo na SGR a shekarar 2017, aikin ya samar da tarin guraben ayyukan yi, ya kuma bunƙasa sashen sarrafa hajojin masanaantun ƙasar. Kaza lika aikin ya raya harkar kasuwanci tsakanin Kenya da sauran ƙasashen duniya. Baya ga inganta fannin fiton manyan kayayyaki ta tashar jiragen ruwan ƙasar.

Bugu da ƙari, bisa hasashen masana, layin dogo na SGR zai riƙa samarwa mizanin awon tattalin arzikin na GDPn ƙasar Kenya kaso 2 zuwa 3 bisa dari a duk shekara.

Layin dogo na SGR mai tsawon kilomita 480, babban aikin more rayuwa ne da aka aiwatar ƙarƙashin shawarar “ziri daya da hanya ɗaya da ƙasar Sin ta gabatar.

Irin waɗannan ayyuka muhimmai da suka kasance jigon haɗin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa, ciki har da ƙasashen Afirka, na nuni ga irin kyakkyawar abota dake tsakanin Sin da ’yan uwanta na ƙasashe masu tasowa, kuma hakan na tabbatar da ingancin alaƙar sassan biyu cikin tsawon lokaci, don haka ba zai yiwu, wani ya iya cimma nasarar ɓata alaƙar waɗannan sassa da suka riga suka amincewa da juna ba!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *