Daga CMG HAUSA
Ana gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidima na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2022 a nan birnin Beijing.
Wasu daga cikin ƙasashe, da kamfanoni da ke halartar wannan baje kolin sun fito ne daga ƙasashen da ke da alaƙa da shawarar “Ziri daya da hanya ɗaya”.
Mahalarta taron daga waɗannan ƙasashe sun bayyana cewa, yin amfani da fasahar zamani, ya samar da damammaki wajen bunƙasa cinikin hidima a duniya, kuma suna fatan yin haɗin gwiwa da ƙasar Sin a fannoni da dama a nan gaba.
A cikin yankin nuna hidimomin al’adu da yawon shakatawa na CIFTIS, ƙasashen da ke da alaƙa da shawarar “Ziri ɗaya da hanya ɗaya”, ciki har da Sri Lanka, sun nuna samfuran al’adun su ga masu sauraro, don ƙara haɓaka musayar ciniki ta al’adu.
Chiranjaya Udumullage, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Sin da Sri Lanka, ya bayyana cewa,
“Yawancin kayayyakin cinikayyarmu suna shiga ƙasar Sin daidai saboda “Ziri ɗaya da hanya daya”.
Ina tsammanin wannan kasuwa tana da girma, kuma yanzu akwai dandamali kamar na watsa shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo, wanda zai taimaka wajen bude kasuwa cikin sauƙi.”
Ya zuwa watan Afrilun bana, ƙasar Sin ta riga ta sanya hannu kan takardun haɗin gwiwa sama da 200, bisa shawarar “Ziri ɗaya da hanya ɗaya” tare da ƙasashe 149 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 32. Zhu Guangyao, babban sufeto a mataki na biyu na sashen cinikin hidima a ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin, ya gabatar da cewa, “A shekarar 2021, jimillar kuɗin kayayyakin ciniki na shige da na fice tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen dake da alaƙa da shawarar “Ziri ɗaya da hanya ɗaya”.
Sun zarce dalar Amurka biliyan 110, adadin da ya ƙaru da kashi 33.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, hakan ya nuna ƙarfin haɗin gwiwar cinikayyar hidima tsakanin ƙasar Sin da waɗannan ƙasashe, wanda kuma hakan zai ƙara haɓaka irin haɗin gwiwar su a nan gaba.”
Mai fassara: Bilkisu Xin