Ƙasashen duniya sun fara mayar da martani kan kalaman Trump na ƙwace Gaza

Bayan furucin shugaban Amurka Donald Trump da ya sha alwashin ƙwace yankin Gaza na Falasɗinu, tuni ƙasashe duniya da ƙungiyoyin Falasɗinawa suka fara mayar da martani na ƙin amincewa da wannan buƙata.

ƙasar Saudiya ta ce ba za ta ƙulla dangantaka da Israila ba idan har babu yankin Gaza, da hakan ke zama martani kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya sha alwashin ƙwace Gaza.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiya ta fitar ranar Laraba, ta yi fatali da duk wani shiri na kwashe Falasɗinawan Gaza zuwa ƙasashe makwafta.

Yarima mai jiran gado, Prince Mohammed bin Salman ya ce sun tsaya kan maganarsu ta cewa basa goyon bayan Trump, kuma babu abinda zai sanya su sauya.

Baya ga haka, ƙasar Chana ta sanar da cewa ba ta amince da tilastawa Falasɗinawa barin yankunansu ba, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Lin Jian ya bayyana.

Shi ma Firaministan Australia Anthony Albanese ya ce manufofin Gabas ta Tsakiya ba za su taɓa sauya wa ba, tuntuni sun amince da zaman Israila a matsayin ƙasa da kuma Gaza a karan kanta, a don haka basa goyon baya.

A gefe guda kuma shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya ce suna faɗa da babbar murya cewa ba su amince da tayin Donald Trump na ƙwace Gaza ba, inda ya ƙara da cewa ba zai taɓa yiwuwa a hana Falasɗinawa ƴancin su ba.

Haka zalika, ƙungiyar Falasɗinawa ta mayar da martani ga Trump, inda ta bayyana ƙarara cewa ba ta goyon baya.

Babban sakaren ƙungiyar Husseini al-Sheikh ya ce ƴa ƴan ƙungiyar sun yi watsi da wannan buƙata ta kwashe su zuwa ƙasashe da ke maƙwaftaka da su. RFI.