Ƙasashen ECOWAS na shirin yanke mu’amala da Ƙasar Mali

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS, za ta ƙaƙaba wa mulkin soji a Mali takunkumi, yayin da ƙasashe mambobin ƙungiyar za su janye dukkan jakadunsu da kuma rufe iyakokin ƙasa da na sama da ƙasar.

Wannan wani ɓangare ne na sakamakon Babban Taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatin ECOWAS da aka gudanar a Lahadin da ta gabata a Accra, babban birnin Ƙasar Ghana.

Babban mataimaki na musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya kan harkokin yaɗa labarai, Laolu Akande ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Ƙasashen ECOWAS za su rufe dukkan iyakokinsu ga ƙasar Mali da janye jakadunsu tare da yin watsi da tsarin miƙa mulkin soja.’

Ya ce bayan nazarin halin da ake ciki a ƙasar Mali a wajen taron, shugabannin yankin sun yi watsi da jadawalin miƙa mulki da sojojin Mali suka gabatar wanda suka ce sam ba za a amince da shi ba.

Kazalika, ECOWAS ta yi wa gwamnatin sojin ƙarin takunkum ciki har da dakatar da duk wata hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashe mambobin ECOWAS da Mali.

Kodayake dai ECOWAS ta keɓe wasu kayayyaki kamar muhimman kayan masarufi da magunguna da kuma kayayyakin kiwon lafiya, musamman kayan lantarki da kuma na yaƙi cutra korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *