Ƙasashen Turai da man fetur a Nahiyar Afirka

Daga BASHIR MUDI YAKASAI

Masana tarihi sun tabbatar da dalilan da suka sa ƙasashen Turai suka kasa barin Nahiyar Afirka duk da cewa sun ba su ’yancin kai, sama da shekaru 60 da suka shuɗe. Duk da cewa sun kwashe sama da shekaru 100, suna waɗari a Afirka suna wawason bayi da amfanin gona tun daga dawa, alkama, auduga da sha’ir da ma’adanai irin su zinare da murjani da azurfa da hauran giwa da jimina da gashinta da kuma turaren wuta.

Da tafiya ta yi tafiya, aka gano Ɗanyen man fetur da gas da kuma dangoginsa, Turawan Yamma da na Amurka sai suka sake share guri suka zauna da sunan abokan ciniki. Kamfanoni Irin su Chevron da Mobil da Total da Shell da kuma BPS suka karaɗe Nahiyar ta Afirka, suke cin karansu ba babbaka. Ta kai ta kawo su ne suke xora shugabanni a fili ko a ɓoye a ƙasashen na Afirka.

Saboda haka ƙasashe na Afirka da suke da man fetur da gas a ƙasarsu kullum suna cikin barazanar zaman lafiya a ƙasarsu.

Dubi Ƙasar Libiya da Misira da Sudan da Kongo da Angola da Zimbagwai da Afirka Ta Kudu da kuma Ƙasar Nijeriya da sauran ƙasashe.

Sababbin ƙasashe da aka fara haƙo ɗanye man fetur da tace shi, kamar Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Ghana, dukkan maƙotan Nijeriya tare da taimakon Ƙasar Sin, wato Chana.

Waɗannan ƙasashen Turai, musamman ma Ƙasar Faransa da Birtaniya da uwar gijiyarsu Amurka, ana ganin suna da masaniyarsu vatagari irin su Boko Haram da IPOB a Nijeriya da ISWAP a Nijar da Burkina Faso da kuma Mali da sauran.

Saboda halayen ’yan ta’adda iri-iri tun daga ‘yan a shajin da varayin dabbobi da yin fyaɗe na ƙananan yara da wawason dukiyar al’umma babu gaira ba dalili kisan bayin Allah ba su ji ba su gani ba sun doshi mutum miliyan ɗaya daga shekara ta 2023 zuwa ta 2022.

Idan za a faɗi gaskiya za ka tarar da hannun waɗannan ƙasashen, domin kuwa su ne suke sayar musu da makamai da ba su horo da kuma kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.

Suna yin haka ne domin korar Chana da Rasha daga Afirka. Su ma waɗannan ƙasashen a na zargin su da su suke ɗaukar nauyin waɗannan ’yan ta’adda ta ƙarƙashin ‘WAGNER’, wanda ya haifar da ruɗani a Ƙasar Mali ta ba wa ƙungiyar nan da ake kira ‘Islamic State-Sahel, wato 15-5 da kuma Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslim (JNIM) da suka fito daga ƙasar ta Mali.

Wani abin takaici a Afirka, su na fitar da gangar ɗanyen man fetur sama da ganga miliyan 10 a kullum, amma talauci da fatara da cututtuka da koma-baya a fannin ilimi da kuma zamantakewa su ne akan gaba.

Duk shugaban da ya qi da tsare-tsaren su da su haɗa shi da mutanansa su yi masa tawaye yadda suka yi wa Kanal Mu’ammar Gaddafi na Ƙasar Libiya, inda suka yara suka kashe shi.

Su na nan su na ƙulle a Afirka Ta Kudu sai sun kawar da shugaban da jama’a suka zaɓa, wai kawai don yana cikin ƙungiyar nan ta BRISAC, wato ƙungiyar da ƙasashen Brazil da Russia da Indiya da South Africa da Chana da kuma Saudiyya, waɗanda dukkan su ƙasashen ne masu hako ɗanyen man fetur da kuma tace shi.

Maganar gaskiya idan wannan ƙungiya ta ɗore ta kuma cimma manufarta, tabbas ƙarshen Amurka ya zo a matsayinta na ’yar sandar duniya.

Tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu Ƙasar Amurka ta ke juya duniya yadda ta ke so, sai abinda ta ke so shi za a yi, ana so ko ba a so, ba don komai ba sai saboda ƙarfin tattalin arzikinta, ga masana’antu ga kuma ƙarfin ɗanyen man fetur da ƙungiyar ta ke fitarwa.

Idan muka yi duba a tsanaki waɗannan ƙasashe da suka kafa BRISAC ƙasashe ne da ruhin duniya yake hannunsu da farko suna da yawan jama’a kusan rabin duniya suna cikin waɗannan ƙasashe, musamman Chana da Indiya da Brazil su kaɗai suna da jumullar mutane sama da biliyan uku daga cikin biliyan takwas na jimillar mutanen duniya.

Kuma kowa ya sani, mutane su ne kasuwa, ba tarin rumfuna ba. Haka ɗabi’ar ƙaura daga wannan guri zuwa wancan, saboda dalilan yaƙe-yaƙe da fatara da yunwa, wanda ’yan Afirka da Asiya da kuma Latin Amurka, wato ƙasashe daga Amurka ta Kudu suke yi a yanzu.

Masu hikimar zance na cewa, ‘Idan za ka haƙa ramin mugunta, to haƙa shi gajere, domin idan ka faɗa za ka iya fitowa’. Amurka da ’yan kanzaginta, ƙasashen Yammacin Turai, su suke rura wutar yeƙe-yaƙe a duniya da sunan aqidar mulkin dimukraɗiyya.

Idan har indiya da Chana da Brazil za su ciyar da kansu, kuma su sama wa ’yan ƙasarsu aikin yi, me zai hana Iran da Iraƙi da Mexico da Argentina da Masar (Egypt) da Nijeriya da Lebanon da kuma Syria ba za su iya ba, bayan suna da ɗanyen man fetur da kuma yawan jama’a?

A mako mai zuwa, idan Allah ya kai mu, za ku ji irin kutungwilar da Ƙasar Amurka da ’yan kanzaginta suke shukawa a Afirka, musammanma a wannan kasa tamu ta Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *