Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Majalisar dokokin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ta ƙaddamar da haɗin gwiwa tare da hukumar ƙidayar yawan jama’a ta ƙasa NPC domin gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a game da ƙidayar jama’a da za a yi a shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar ranar Talata, ya jaddada cewa akwai muhimmiyar rawar da sahihan bayanan ƙidayar jama’a ke takawa wajen ciyar da ɓangarori masu muhimmanci a cikin al’umma.
Falgore ya jaddada ƙudurin majalisar dokokin Kano na haɗin gwiwa da hukumar ƙidaya ta ƙasa a Kano domin ƙarfafa hanyoyin wayar da kan jama’a domin ƙidayar da ke tafe a faɗin kasar nan.
Kazalika, Falgore ya yaba da ƙoƙarin Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa na farfaɗo da hukumar a Kano, sannan ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan majalisar dokokin Kano wajen haɗa kai da hukumar ƙidaya ta ƙasa a Kano wajen ganin an aiwatar da ita cikin nasara da kwanciyar hankali.
Daga nan ne dai, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya bayyana jin daɗin sa da irin tarbar da shugaban majalisar ya yi masa, sannan ya yi kira ga al’umma da su taimaka musu wajen ganin sun cika aikin da aka ɗora masu a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙokarin gudanar da ƙidayar fasahar sadarwa ta zamani da bata taɓa yin irinta ba.
Babbar manufar ziyar dai shi ne haɗin gwiwa da masalisar domin ƙara wayar da kan al’umma kan ƙidaya domin amfanin al’ummar Jihar Kano.