Ƙin canji ya sa ni sauka daga Darakta Janar na ƙungiyar gwamnonin APC – Dr. Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Darakta Janar na Ƙungiyar Gwamnonin APC, Mohammed Salihu Lukman, ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga ƙungiyar ta PGF. 

Murabus ɗin nasa a ranar Litinin ya zo ne sa’o’i 24 bayan ganawar gwamnonin jam’iyyar APC a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi a daren Lahadi, a daidai lokacin da APC ke cikin tsaka-mai-wuya na rashin tantance ranar da za ta zaɓi sabbin shuwagabannin ta.

Manhaja ta ruwaito a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Lukman ya ce ya guje wa yin tsokaci ne kan murabus ɗin nasa saboda jam’iyyar ba ta riga ta amince da hakan ba. 

“Zan iya tabbatar mu ku da cewa da gaske ne na yi murabus kuma na miqa takarda ga Abubakar Bagudu. Na nisanta kai na daga yin tsokaci ko fitar da wata takarda a kan lamarin ne saboda ina jiran amincewar su. 

“Na yi magana da shugabannin jam’iyya, ‘yan uwa da abokan arziki, kuma na yi musu bayanin cewa gaskiya ne na yanke hukuncin murabus daga wannan muƙamin. 

“Abun sha’awa, bayan jin labarin murabus ɗina, da yawa daga cikin shugabanni da mambobi sun kira ni domin nuna damuwar su. Ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar wanda ya kira ni shi ne Tinubu. Ya gayyace ni a ranar 17 ga watan Nuwamba.

 “Ya jinjina min kan yadda na dinga gangamin ganin gyaran jam’iyyar kuma ya nuna mamakin sa kan yadda wasu mambobin jam’iyyar ke caccaka ta.” 

Lukman ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya assasa kafa kwamitin zaɓen shugabanni, inda ya ƙara da cewa hankula sun fara tashi yayin da kwamitin suka gagara yin zaɓen sabbin shugabanni. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *