Ƙin samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro

Daga NAJEEB MAIGATARI

Kwanakin baya tattaunawa ta haɗa ni da wani aboki na, sai yake ce mun ai ana sane aka ƙi samar da rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro (Malaria) duk da irin yanda kuwa cutar ta addabi musamman ƙananun yara da yanda ta ke kashe su. Har ya jefo mun wata tambaya; me yasa ba a damu da samar da rigakafin ‘Malaria’ ba, amma aka damu mutane da yi mu su rigakafin cutar shan inna (Poliomyelitis) duk da cewar yanzu ba a fama da ita?

Maganar gaskiya shi ne a wancan lokacin ba ni da amsar tambayar shi, saboda ban san komai akan cutar ‘Malaria’ ɗin ba; ƙarewar ta ma na yarda da batun shi cewa su Bill Gates su na da wani ƙulli ne akan ‘yan Afrika ya sa suke ta ɗirka mu su allurar rigakafin cutar shan inna (Polio a takaice). Yanzu kamar shekaru uku kenan baya da yin wannan tattaunawar.

Amma daga baya, na zo na san abubuwa daidai gargwado akan cutar (Malaria) da kuma kwayar halittar da ke haddasa ta (Plasmodium parasite)- koma bayan sauro (mosquito) da mafi yawan mutane suke zaton shi ke haddasa cutar. Kuma fahimtar yanda su waɗannan ƙwayoyin cuta su ke, ya sanya ko an ɗauki shekaru ɗari ba a iya samar da rigakafi akan cutar da su ke haddasawa ba zan yi mamaki ba (haka ma duk wanda ya san yanda su ke).

Mafi yawan halitta su na canja ɗabi’ar su ne daidai da muhallin da su ka samu kan su a ciki: da zarar muhallin da su ke ciki (misali jikin mutum) ya canja da nufin ya murƙushe su, su ma za su canja ɗabi’ar su yanda za su tsallake wannan barazanar- abun da ake kira da ‘evolutionary adaptation’. Wataƙila, mafi shahara kuma mafi sauƙin misalin da za mu fi ganewa shi ne yanda hawainiya (chameleon) ke canja kalar jikin ta saje da muhallin da ta ke don kariya daga duk wani abun da zai iya cutar da ita. Sai ya gane ta zai iya kashe ita ko?

Haka zalika, su ma wasu kwayoyin halittar ‘parasites’ su na da hanyoyi da dama da su ke bi wajen tsallake tare da kare kan su daga barazanar sojojin jikin mu (wanda su ke bada garkuwa ga cututtuka). Ɗaya daga cikin irin wadannan hanyoyin shi ne “epigenetic regulation”.

A sassauƙar Hausa, bari na kira shi da yanda su ke yin dabara ta hanyar canja wani ɓangare na taswirar jikin su (amma ba halittar su ba) don ɓoyewa daga mamayar sojojin jikin wanda su ka kama. Hakan zai sanya su dauki lokaci mai tsawo su na illata mutum.
Ga kwayar halittar da ke haifar da cutar ‘Malaria- musamman jinsin ‘Plasmodium Falciparum- duk sanda ta ga dama ta na iya kashe ko kunna wani ‘surface protein’ da ke jikin ta (wanda dole sai sojojin jiki sun gan shi ne sannan za su iya kai mata farmaki).

Matuƙar ta kashe shi, sojojin ba za su iya ganin ta ba, duk da cewa tana nan ta na ta hayayyafa son ran ta a cikin jiki.
Babban shu’umancin ta kuma shi ne ta hanyar wani sinadari da ta ke saki a jikin mutum ta na iya hana a samar da wasu kalar sojoji na musamman (dendritic cells) da su ke taimakawa wajen gane ƙwayar cuta (recognition) da kuma yaqar ta- wannan ya sha bamban da na HIV da ke kashe wasu kalar sojojin da ke yaqi a jiki, kamar yanda na yi bayani a rubutun da ya gabata.

Saboda haka, abubuwa biyu ne: na farko, ɓoye kan ta da take yi ta yanda sojojin cikin jiki ba su iya ganin ta; na biyu, hana a samar da wasu kalar sojojin na musamman (dendritic cells) wadanda su ne ke gane tare da daukar kwayar cuta da zarar ta shiga jikin mutum su kai ta ga wasu kalar sojojin na daban waɗanda za su kashe ta.
Akwai sauran shu’umanci kala-kala da ta ke yi, amma waɗannan guda biyun su ne ke da alaƙa da maganar da za mu yi nan gaba, Inshaa Allah!

Wannan na daga cikin dalilin kuma da ya sanya har zuwa yau ɗin nan sojojin jikin mutum ba su iya samar da garkuwa sosai (sustained immune response) ga cutar ‘Malaria’ (although akwai wadansu cututtuka da ke ɗan bada kariya ga cutar).

Shi ya sanya mutum zai kamu da cutar ‘Malaria’ ya sha magani ya warke, amma idan da ace zai sake kamuwa da ita wani lokacin sai a ga ya sha wahala sosai, wasu ma kamar ba za su yi rai ba. Ballantana kuma ƙananan yara da ta zama barazana ga rayuwar su.

Wannan ya sanya wasu mutanen a gari ke cewa ba a warkewa daga cutar ‘Malaria; amma a haƙiƙanin gaskiya shi ne rashin samar da garkuwar nan sosai yanda ya kamata ga ƙwayar halittar (Plasmodium parasite) shi ne babban abun da ya ke haddasa wannan yawan kamuwa da ita ɗin lokaci zuwa lokaci- kuma kowane lokaci idan mutum ya kamu za ta iya wahalar da shi.

Da ya ke cutar ‘Malaria’ kowa ya san ta, qila ma mutum ya taba yin ta; wannan zai zama matashiya kafin a rubutu na gaba Inshaa Allah mu kai ga amsar tambayar aboki na: me yasa har yanzu babu rigakafin Malaria? Da gaske ne an ƙi samar da shi ne don a bar ‘yan Afrika su mutu?

Zan ci gaba, Insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *