Ƙofar mu a buɗe take domin karɓar shawarwari don kyautata tsarin muhalli a Dala – Ummi Alasan 

Daga IBRAHUM MUHAMMAD a Kano

Mai bai wa Shugaban ƙaramar Hukumar Dala shawara akan muhalli, Hajiya Ummi Alasan ƙofar Ruwa ta  bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati  Shehu Wada  Sagagi da ‘yan majalisun Dala da Kwamishina Ibrahim Namadi da jagoran Kwankwasiyya na Dala ɗayyabu Ahmad Maiturare bisa goyon bayansu wajen ba ta muƙamin.

Ta ce sun samu shugaban ƙaramar hukumar Dala Suraj Imam Mutum ne jajirtacce mai ilimi na zamani da na addini da yake yin ƙoƙarin haɗin kai a wannan tafiya da suke ta Kwankwasiyya amana.

Hajiya Ummi Alasan Kofar Ruwa ta yi nuni da cewa matsayin da aka bata ta mai bayar da shawara akan muhalli, an sanya ƙwarya a gurbinta, domin ita dama bata son taga ƙazanta ko yaya take ko a unguwar su takan fito da yara a yi aikin gayya na kwata a gyara a kwashe.

Ta ce za su bada shawara ga shugaban ƙaramar hukumar Dala, Hon. Suraj Imam domin ganin an samu nasarar kyautata tsarin muhalli da bin doka, hakan zai taimaka wajen tabbatar da binne ƙa’ida.

Ta ƙara da cewa yanzu wannan muƙami ya ƙara mata ƙwarin gwiwa da za ta bada shawara akan inda taga yakamata  a gyara da inda  za a yi wani abu muhimmi da zai taimaki al’umma komai ƙanƙantarsa don haka ta ji daɗi da wannan dama da aka bata.

Hajiya Ummi Alasan ƙofar Ruwa ta yi kira ga al’ummar Dala akan su bata haɗin kai da goyon baya kuma ƙofarta za ta zama a buɗe a zo a bata shawara a koya mata idan an ga ta yi kuskure a sanar da ita domin ta gyara.