Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An samu taƙaddama mai zafi a Majalisar Dattawa yayin da Sanata Ali Ndume ya yi martani ga Mataimakin Shugaban Majalisar, Barau Jibrin, kan ƙoƙarin gayyatar ƙwararru kan haraji da jami’an gwamnati zuwa zauren majalisa ba tare da sanarwa ba.
Rikicin ya ta’allaƙa ne kan Dokokin Gyaran Haraji, inda wasu ‘yan majalisa daga yankin arewa suka bayyana rashin amincewarsu.
Rikicin ya fara ne lokacin da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Opeyemi Bamidele, ya sanar da wani ba-zata game da dakatar da ajandar ranar don bai wa ƙwararrun haraji da jami’ai, ciki har da Shugaban Hukumar FIRS, damar gabatar da jawabi ga ‘yan majalisa kan Dokokin Gyaran Haraji da ake taƙaddama kansu.
Duk da haka, Sanata Abdul Ningi ya nuna adawa da hakan bisa ƙa’idojin Majalisar Dattijai. Ya ce ƙa’idojin ba su ba da izini ga kowa ya yi magana a zauren majalisa ba sai tsoffin Shugabannin ƙasa, tsoffin Shugabannin Majalisar Wakilai, da tsoffin sanatoci.
Ningi ya jaddada cewa irin wannan bayani daga ƙwararru ya dace a yi shi ne a matakin kwamitocin majalisa, ba a taron majalisar gaba ɗaya ba, kasancewar dokokin majalisar ba su amince da irin wannan ba.
Sanata Barau Jibrin, wanda ke jagorantar zaman majalisa, ya mayar da martani ta hanyar cewa Dokokin Gyaran Haraji suna da muhimmanci ga ƙasa kuma tuni Majalisar Wakilai ta yi aiki a kansu.
Ya yi bayanin cewa bai wa ƙwararru damar yin magana a zauren majalisar zai taimaka wa ‘yan Nijeriya su fahimci abinda dokokin suka ƙunsa.
Daga nan sai ya yi fatali da maganar Ningi.
Sanata Ndume, cikin ɓacin rai, ya faɗa wa shugaban zaman majalisar da cewa, “Za ku iya cimma muradinku, amma ni zan yi magana.”
Ya kuma ƙara da cewa, “Za ku iya amfani da guduma, amma ni zan yi amfani da muryata.”
Rikicin ya daɗa ta’azzara lokacin da Sanata Ndume, cikin takaici, ya jagoranci wasu ‘yan majalisa daga arewa wajen ficewa daga zaman majalisar a matsayin alamar rashin jin daɗi game da take dokar majalisa.
Bayan roƙo daga Shugaban Marasa Rinjaye da wasu abokan aikinsa, Ndume da sauran sanatocin da suka fita suka koma zauren majalisa.
Da suka dawo, Ndume ya sake ɗaukar mataki ta hanyar yin magana bisa ƙa’ida, yana neman Mataimakin Shugaban Majalisa Barau ya ba shi haƙuri saboda zarginsa da yin magana ba tare da hujja ba.
Amma Barau ya sake yi masa fatali da maganarsa, sannan aka ci gaba da bai wa ƙwararrun haraji damar yi wa sanatoci bayani kan Dokokin Gyaran Haraji, duk da adawar da aka yi.