Ƙudirin gyaran haraji: Majalisar Dattawa ta umarci kwamiti ya dakata da aiki, ta samar da wani don magance matsalolin da ke ciki

Daga BELLO A. BABAJI

Shugabancin Majalisar Dattawa ta umarci kwamitinta na kuɗi da ya dakatar da aiki akan ƙudirin neman gyaran haraji har zuwa bayan kammala babban zama da Antoni Janar na Ƙasa, AGF.

Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar, a ranar Laraba inda ya ce an samar da kwamiti na musamman don warware matsalolin da suka haifar da muhawara acikin al’ummar ƙasa game da ƙudirin.

A ranar Alhamis ne kwamutin zai gudanar da zaman tattauna batun don samar da mafita game da muhawarar da ƴan majalisa da masu-ruwa-da-tsaki suke yi a kai.

Sannan, majalisar ta sanar da shirin gudanar da zama na musamman ƙarƙashin jagorancin shugaban ɓangaren marasa rinjaye don warware ɓangarorin da aka yi saɓanin kuma ake muhawara akan su.

Za a gudanar da zaman ne saboda tabbatar da cewa an yi la’akari da maslahar ƙasa da cimma matsaya.

Mambobin kwamitin na musamman sun haɗa da; Abba Moro a matsayin Shugaba,
Tahir Monguno, Aliero Adamu, Kalu Orji, Dickson Seriake, Zam Titus, Yahaya Abdullahi, Adeola Solomon, Sani Musa, da Abiru Mukhail da kuma shugabancin Majalisar.