Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sanar da sauya wajen ɗaurin auren ƴarsa daga Jihar Kano zuwa birnin tarayya Abuja.
Hakan na zuwa ne sakamakon sanarwar da wasu matasan Arewa suka fitar don hana sanatoci shiga kowacce jiha ta Arewa, tare da cewa matukar suka yi kunnen ƙashi suka shigo, to za su yi musu ruwan duwatsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Hakan ba zai rasa nasaba da fusatar da al’ummar Arewacin Nijeriya suka yi ba kan kudirin dokar sauya fasalin haraji da ake kallon jihar Lagos ce za ta fi cin moriyarsa.
Sanata Barau, ya ce dan kare baƙi na gida da na waje, ya sa dole aka mayar da ɗaurin auren zuwa Abuja.
A ranar 13 ga watan Disamba ne za a ɗaura auren ƴar gidan tsohon Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da kuma ɗan Sanata Barau Jibrin (Maliya).