Ƙudirin haraji: Ba rigima nake da Tinubu ba, so nake a ƙara tuntuɓa – Zulum

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi ƙarin haske game da tsokacin da ya yi kan ƙudirorin neman gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisa.

Ya ce kaɗai abin da ya ke kira akai, shi ne a faɗaɗa tuntuɓa da nazari game da lamarin, ya na mai cewa ba rigima ya ke yi Shugaban ƙasar ba.

A baya ne Zulum ya zargi cewa Jihohin Legas da Ribas ne kaɗai za su mori kwaskwarimar da Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin yi wa haraji a Nijeriya, kamar yadda ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na ‘channels’.

Zulum ya ce matsayar ta ginu ne akan bincike da nazari da gwamnonin Arewa suka yi.

Gwamnan ya kuma bayyana dalilan da suka sa gwamnonin Arewa suka shawarci Tinubu ya dakata da fafutukarsa ta kwaskwarimar harajin, inda ya ce la’akari da bincikensu, sun gano cewa Arewa ba za ta yi nasara ba matuƙar aka zartar da su.

Acikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkar labarai, Dauda Iliya ya fitar, Zulum ya ce kaɗai abin da ya nema shi ne a faɗaɗa tuntuɓa, wanda kuma ya na ɗaya daga cikin tsare-tsaren duk wata ƙasa ta demokraɗiyya.

Gwamnan ya nuna damuwa kan dokar harajin VAT da ya wakilci kaso 60 na kuɗin shiga, wanda ya ce jihohi ƙalilan ne za su amfana da shi.

Farfesa Zulum ya shawarci da a samar da daidaito acikin abin da kwaskwarimar ta ƙunsa ta yadda ba za mayar da wani ɓangare saniyar ware ba game da ƙaddamar da ayyukan ci-gaba.