Daga USMAN KAROFI
Ƙasa da mako guda bayan rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin Nijeriya sun yi barazanar hana ‘yan majalisar tarayya tikiti na zaɓen shekarar 2027 saboda goyon bayansu ga ƙudirin gyaran haraji na shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wasu daga cikin ‘yan majalisar sun musanta wannan zargi.
A ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024, mataimakin kakakin najalisar wakilai, Mista Philip Agbese, ya bayyana cewa wasu gwamnonin suna yi wa ‘yan majalisar barazana da hana su tikitin komawa kan kujerunsu idan ba su janye goyon bayansu ga ƙudirin gyaran haraji ba.
Sai dai wasu ‘yan majalisar sun bayyana cewa gwamnonin ma yanzu suna goyon bayan ƙudirin, saɓanin abin da aka fara bayyanawa.
Ƙudurin gyaran dokar harajin, wanda aka tsara bisa shawarar Kwamitin Shugaban Kasa kan gyaran haraji ƙarƙashin jagorancin Taiwo Oyedele, sun haɗa da samar da doka mai tsara tsarin haraji a Ƙasa, gyaran dokokin gudanar da haraji da kuma kafa hukumar haraji ta Nijeriya.
Wannan zai maye gurbin dokar hukumar FIRS da kuma kafa kotu mai lura da batutuwan haraji. Duk da haka, gwamnonin jihohin arewa 19 sun nuna rashin amincewa da canjin tsarin rabon VAT daga yawan jama’a zuwa asalin samuwar kuɗaɗen, suna ganin hakan zai ba wa yankin kudancin ƙasar fifiko.
Ɗan majalisa mai wakiltar Ehime Mbano/Ihitte/Uboma/Obowo daga Jihar Imo, Chike Okafor, ya musanta zargin, yana mai cewa gwamnan jiharsa yana goyon bayan ƙudirin harajin. Ya ƙara da cewa, “Gwamnan mu tsohon ɗan majalisa ne mai shekaru takwas a majalisa, kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC. Bai taɓa mana magana kan ƙin goyon bayan ƙudirin ba.” Haka shima Babajimi Benson, ɗan majalisar Ikorodu, ya ce ƙudirin gyaran harajin na da amfani sosai ga ƙasa, kuma duk gwamna da ya karanta dokokin zai goyi bayansu.
A yayin da ƙudurin harajin za su fara samun tattaunawa a gaban majalisar a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba, wasu ‘yan majalisa kamar Joshua Gana daga Jihar Neja da Alex Ikwechegh daga Abia sun bayyana cewa babu wata barazana da za ta hana su yin abin da ya dace da muradin al’umma. Gana ya ce, “Allah ne ke ba wa mutum shugabanci, ba wai gwamnonin ba,” yayin da Ikwechegh ya musanta samun wata barazana daga gwamnan jiharsa kan dokokin.