Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya nuna damuwa kan ƙudirin neman yi wa haraji kwaskwarima, inda ya ce hakan zai yi illa ga yankin Arewa da suaran sassan Nijeriya.
Zulum ya bayyana haka ne a yayin hira da BBC Hausa a ranar Juma’a inda ya kwatanta shi da ƙudirin masana’antar fetur wadda sai da ta ɗauki kusan shekaru 20, ya na mai cewa akwai buƙatar a yi zurfin nazari game da batun.
Babagana Zulum ya zargi cewa ƙudirin zai haifar da matsaloli ne ga shiyyoyin Nijeriya inda ya yi watsi da miƙa shi ga majalisa da aka yi domin tantancewa.
Ya kuma yi zargin cewa akwai wasu da ke ruɗar Shugaba Bola Tinubu kan cewa Arewa ba ta goyon bayan gwamnatinsa, ya na mai cewa suna da fahimtar cewa ƙudirin zai tarwatsa Arewa.
Gwamnan ya ƙara da cewa, matuƙar ƙudirin ya tsallake matakin tantancewa, jihohin Arewa za su fuskanci kalubale wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba har da biyan albashi.
Ya ce lallai ba sa goyon bayansa, haka ma Jihar Legas sakamakon koma-baya da hakan ka iya haifarwa acikin al’umma.
A ranar Alhamis ne Majalisar Dattijai ta gabatar da karatu na biyu ga ƙudirorin haraji guda huɗu inda ta miƙa su ga kwamitinta na kuɗi tare da umartar sa da ya dawo da su nan makonni shida.