Ƙudurinmu shi ne tallafawa kowa ne ɓangare a ƙaramar Hukumar Tarauni – Hon ADS

Daga RABIU SANUSI a Kano

ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar Hukumar Tarauni, Alh Kabiru Dahiru Sule (ADS), ya bayyana ƙudurinsa na inganta harkokin lafiya, ilimi, da tallafawa matasa don samun cigaba mai ɗorewa a yankin Tarauni.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Tarauni Adamu Iliyasu Hotoro ta fitar, ya ce Alh. Kabiru ɗahiru Sule ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa, wanda suka hada da Gina Cibiyar Kula da Lafiya a mazabar Gyadi-Gyadi Arewa, gina hanyar magudanan ruwa a mazaɓar Gyaɗi-Gyaɗi Arewa, gina ɗakin haihuwa da bandaki a mazaɓar Gyaɗi-Gyaɗi ta Kudu.

ɗan majalisar Kabiru Dahiru ya ce ya ƙuduri aniyar tallafawa ɓangaren lafiya, ilimi da samar da damarmaki ga matasa domin dogaro da kai. Wannan shine ginshiƙin ci gaban al’umma, kuma zan yi ƙoƙari don ganin yankin Tarauni ya ci gaba yadda ya kamata a wannan lokacin.

A jawabinsa tun da fari shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Alh. Ahmed Ibrahim Muhammad sekure Wanda ya nuna farin cikin sa kan yadda Dan majalisar jiha Alh. Kabiru Dashiru ya fara ƙaddamar da manyan ayyukan raya ƙasa faɗin mazabun goma dake yankin inda shugaban ƙaramar hukumar ya bada tabbacin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da ɗan majalisar don tabbatar da an samar da sabuwar Tarauni. 

Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya yi kira ga jama’ar yankin da su rungumi waɗannan ayyuka tare da bada cikakken haɗin kai wajen kula da su. 

Daga nan ya gode wa gwamnatin jiha ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf da jagoran Kwankwasiyya na ƙasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da dukkan masu ruwa da tsaki bisa goyon baya wajen tabbatar da ayyukan raya a ƙasa a faɗin yankin bakiɗaya.

Taron ya samu halartar Shugaban Jami’iyar NNPP, kansiloli da masu bai wa shugaban ƙaramar hukumar shawara.