Ƙunci da kaɗaici da kewar mahaifina ne silar fara rubutuna – Faridat Mshelia

“Na fi son yin rubutu lokacin da nake cikin ɓacin rai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Faridat Hussaini Mshelia, wata matashiyar marubuciya ce daga ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja, tana cikin marubutan da sunan su ke amo, musamman tsakanin marubuta na onlayin, ta rubuta littattafai guda goma da gajerun labarai da dama. Labaran ta sun fi mayar da hankali ne akan zamantakewa da faɗakarwa kan yadda rayuwar matan Musulmi za ta inganta, a dukkan wasu fannoni na rayuwa. Daga cikin littattafan da ta rubuta irin su Mutuncinki ‘Yancinki, Sanadin Facebook, da Bestin Mijina, akwai darussa masu yawa na gyara kayanka, don kyautata tarbiyyar al’umma. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya samu zantawa da ita, kuma a cikin tattaunawar da suka yi ne take gaya masa dalilin da ya sa ta fara rubutun littafi, wanda ke da alaƙa da rasuwar mahaifinta. Allah Ya ƙara haskaka makwancinsa, amin. 

MANHAJA: Ko za mu fara da sanin cikakken sunan marubuciyar?

FARIDAT: Assalamu alaikum warahmatullah. Sunana Faridat Hussaini Mshelia wacce duniyar rubutu ta fi sani da Ummu-Jidda Suleja. 

Za mu so mu san wani abu daga tarihin rayuwarki?

An haife ni ne a ƙaramar Hukumar Suleja da ke Jihar Neja a shekarar 1995. Na fara karatuna a makarantar firamare ta Shu’aibu Na’ibi da ke Suleja, makarantar da ka fi sani da Bakin Kasuwa, inda na kammala a shekarar 2006. Sannan na shiga makarantar Sakandire a shekarar 2007, a wata makaranta mai suna Model Commercial College, inda na yi aji biyu a nan, sanadiyyar tashinmu daga cikin garin Suleja zuwa wani gari da ake kira Gauraka wadda ya ke daf da Dutsen Zuma. An sake sanya ni a wata makarantar inda na gama aji uku har na shiga SS1, sai kuma aka cire ni aka mayar da ni makarantar sakandiren Gwamnati ta Model School a nan Suleja, a nan ne na samu shaidar kammala sakandire ɗina. Na kuma fara gabatar da karatun NCE ɗina a shekarar 2012, amma ban yi nisa ba sai aka cire ni aka yi mini aure, saboda rashin mahaifina da na yi a wannan tsaikon.

A fagen karatu na addini kuwa tun ina da shekara 11 na sauke Alƙur’ani Mai Girma, bayan nan na ƙara yin sauka da ƙira’ar warshu, bayan an koyar da ni yadda ake rubutu a allo, domin da bagdadi muka yi karatu. Sannan na cigaba da karatun littattafan addini, har na sauke wasu daga ciki. Kawo yanzu ina kan neman ilimi kamar yadda Annabi ya ce, “Neman ilimi farilla ne akan kowanne Musulmi da Musulma.”

Kamar yadda na faɗa a baya, ina da aure da yara guda 5, sai dai ɗana na farko Allah Ya masa rasuwa.

Yaushe kika fara rubutu kuma mene ne silar fara rubutun?

A shekarar 2011 na fara rubutu sanadin rashin mahaifina da na yi. Silar fara rubutuna dai bai wuce son na sanya mahaifiyata farinciki ba, saboda a lokacin mun rasa mahaifinmu wanda ya kasance shi ne bango abin jinginar mu, kuma fitila mai haska mana rayuwa. To, yayin da muka tsinci kan mu a wannan yanayin sai muke taruwa a ɗakin babarmu muna yi mata hira, a duk bayan sallar isha. Kowa burinsa shi ne ya mantar da ita damuwar ta. Ni sai na zaɓi hanyar rubuta labari, kuma cikin ikon Allah, idan na rubuta sai ƙannena da ƙawayensu su yi ta tafa mini suna zuga ni akan ya yi daɗi. Ganin farincikin su yana sanya ta farinciki don haka sai ka ga ta warware ana ta hira. Don haka a taƙaice, ƙunci da kaɗaici da kewar mahaifina shi ne silar fara rubutuna.

Yaya alaƙar ki take da marubuta da masu karanta rubutunki?

Kyakykyawar alaƙa ce tsakanina da marubuta mazan su da matan su, masu buga littafi da na onlayin ‘yan’uwana. Ina da ƙawaye, ƙanne, yayu, aminai, har ma da masoya a cikinsu.

Makaranta kuwa muna zumunci da su sosai, wasu na kiran wayata, wasu na kawo mini ziyara har gida. Daɗin daɗawa ma har uwa na yi a onlayin wacce ta zama mini garkuwa a zahiri da baɗini. Don haka ina da kyakkyawar alaƙa da marubuta da makaranta. Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya.

Waɗanne hanyoyi kike bi wajen zaɓar jigo idan za ki yi rubutu?

Hanyoyin suna da yawa, amma magana ta gaskiya na fi zaɓar jigon rubutu akan abin da idona ya gani, ko wanda ya ke ci mini tuwo a ƙwarya. Babban misali shi ne, ni a garin da nake rayuwa, gari ne da ya haɗa mabambantan ƙabilu, masu al’adu daban-daban, a yayin da na ga matar Malam Bahaushe tana yi wa mijinta wani abu na rashin kyautatawa sai in ji babu daɗi. Don haka sai in samu damar da zan haska musu rayuwar wata ƙabila wacce ta ke cikin wahala, domin su san su kukan daɗi suke yi kamar dai yadda ya kasance a littafina na Bestin Mijina. Abin da ya faru da gaske a gabana, ko na ji da kunnena, ko na yi bincike na tabbatar gaskiya ne. A nan nake samun jigo a yayin da duk zan yi rubutu.

A wanne yanayi kika fi jin daɗin yin rubutu, kuma me ya sa?

Idan raina yana ɓace na fi son in amayar da fushina ta hanyar yin shiru, sannan in samu wuri marar hayaniya a wannan lokacin na fi jin daɗin yin rubutu. Dalili kuwa na fi nutsuwa sannan hankalina ya kan kwanta in ji ni a wata duniya mai mantar da ni damuwa.

Duk wani abu na rayuwa tattare yake da ƙalubale da nasarori, ko za mu iya sanin wasu daga cikin nasarori da ƙalubale da suka shafi kasancewarki marubuciya?

Tabbas haka ne amma ni magana ta gaskiya na shiga harkar rubutun adabi da ƙafar dama, domin tun daga gida ma’ana cikin ahalina na samu sun karɓi abin hannu bibbiyu. Don haka babu wani sahihin ƙalubale da zan ce na fuskanta wanda zan iya bayyana wa duniya. Nasarorina kuwa sun tsallake tunanina, don haka ba na hangen wata matsala. Har kullum babu abin da nake yi sai godiya ga Allah, da Ya raya matacciyar da take da burin zama lauya ta zama marubuciyar da wasu ke burin koyi da ita. Don haka nake cewa, “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah ala kulli halin!” Kuma ina mai ƙara godiya gare Shi da tarin ni’imomin da Ya yi mini waɗanda ba za su lissafu ba. Don haka na ke cewa nasarata ta shafe dukkanin wani ƙalubale.

Babban dalilina kuwa shi ne, a shekarar 2020 na fara shiga gasar Aminiya ta Daily Trust, kuma cikin ikon Allah sai na samu kira akan labarina ya shiga ɗaya daga cikin waɗanda suka cancanci yabo. Har ma an buga labarin tare da bani satifiket. Tabbas wannan babbar nasara ce wadda ta ƙarfafa mini gwiwa tare da sanya wa na shiga harkar rubutu gadan-gadan, don a baya ban san kowa ba, kuma babu wanda ya sanni.

Nasara ta biyu ita ce, fara shiga gasar Hikiyata ta mata zalla wadda BBC Hausa ke shiryawa a duk shekara, inda ina tura wa Malam Jibrin Rano labarina akan ya duba mini sai na ji yana ta jinjina mini, har ma bayan an fitar da sakamako ya ce in yi maza in je in duba, amma sai na tarar da babu sunana. Sam ban karaya ba, tunda da shi da yayana sun gwada mini zan iya, kuma suna ƙarfafa mini gwiwa. Haka na cigaba da shiga, inda labarina ya taɓa zuwa na 5 a gasar mata zalla na Hikayata. tabbas wannan nasara ta faranta mini rai kuma ta ƙara ƙarfafa mini gwiwa.

Sai nasarar da na samu a Gasar ɗangiwa inda muka yi kunnen doki da wasu ‘yan’uwana marubuta, inda na zo ta huɗu na kuma samu kyautar zunzurutun kuɗi har Naira dubu ɗari, da wadda Gwamnan Jihar Katsina ya ƙara mana kyautar dubu hamsin.

Amma babbar nasarata a harkar rubutu ita ce haɗuwa da mutanen kirki, don wasu suna jina a jininsu tamkar ciki ɗaya muka fito. Ina da masu yi mini faɗa, don haka, Alhamdulillah.

Tsakanin rubutun littafi da gajeren labari wanne ki ka fi jin daɗin rubutawa?

Yanzu da na zama maƙyuyaciya gaskiya gajerun labarai na fi rubutawa. Wannan dalilin ne ma ya sa nake da son shiga gasanni, saboda cikin taƙaitattun kalmomi za ka dunƙule saƙonka kuma ya isa kunnen dubannin mutane.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu da taƙaitaccen bayani game da labarin?

Na rubuta labarai za su kai guda goma. Daga ciki akwai ‘Mutuncinki ‘Yancinki’, ‘Auren Jari’, ‘Ita Ce Sila’, ‘Soyayya Lokacin Kulle’, ‘First Ramadan With Habibi’, da ‘An ƙi Cin Biri’, ‘Bestin Mijina’, da kuma ‘Soyayyar Facebook’. 

Littafin ‘Mutuncinki ‘Yancinki’ shi ne littafina na farko, na rubuta shi ne akan muhimmancin sanya hijabi da suturta jiki, inda jigon labarin ya kasance akan wata ɗiyar mai kuɗi da ɗiyar Malam Shehu. Jarumar labarin wacce ta fito daga gidan masu hannu da shuni ta kasance ɗiya mai tarbiyya saboda dace da ta yi da uwa tagari, saɓanin ɗiyar gidan talaka wacce ta yi rashin dace da uwa wacce ta zama silar lalacewar tarbiyyarta, duk kuwa da kasancewar mahaifinta mutumin kirki ne. Yayin da wata kakar ta ke ƙoƙarin ɗora ta akan tudun da za ta samu tsira, ashe tufka take yi mahaifiyar ɗiyar na warwarewa. Dalilin hakan ta sarayar da mutuncinta ga wani ɗan shaye-shaye. Wannan ce lokacin ta gane ashe mace ta kama mutuncinta shi ne kaɗai ‘yancin da take da shi a wurin namiji, kamar yadda ta ga ɗiyar attajiri ta yi rayuwa mai kyau, duk da ta zama ma’abociyar sanya hijabin da ta ke ɗaukar shi a matsayin rashin wayewa.

Sai kuma littafin ‘Bestin Mijina’, labari ne da na gina shi akan wata ƙabila da ta fito daga yankin arewacin ƙasar nan. Na gina labarin ne kacokam akan wahalar da wasu matan ƙabilu ke sha tare da faɗi tashin da suke yi saɓanin matan Hausawa da ke kwance a inuwa maza na fita suna kawo musu suna rainawa. Na kuma taɓo hangen da wasu matan Hausawan ke yi akan matan ƙabilu ta yadda zai yi wahala ka ga an yi musu kishiya amma suna da kishiyoyi a waje bila’adadin sun sani kuma babu yadda suka iya da mazajensu. Hasalima, tauraruwar littafin har gadonta na Sunnah mijinta yana kawo mata, bayan ita ce ta ke ciyar da shi, ta shayar da shi, ta kuma ɗauki ɗawainiyar ‘ya’yansu, amma ban da kyara da hantara babu abin da yake yi mata, duk da tarin biyayyar da take yi masa.

A ɓari guda, labarin kuwa wurin da na taɓo matar Malam Bahaushe har maita ta saya da kuɗinta, domin ta hana mijinta ƙara aure, bayan ita ce ta gaza, ta kasa sayen shi da kyautatawa, sai izza da nuna isa da take yi masa. Bestin mijina dai ita ce silar raba auren Falmata da ta zamto masheƙiyar zuciyar mijin Lami mayya. Labarin dai ya taɓo ababe masu motsa zuciya. Alal’haƙiƙa ma wani ɓangare na labarin ya faru da gaske! 

Akwai kuma littafin, Sanadin Facebook, wanda labari ne da na gina shi akan illar auren dole da rashin ja a jika da wasu mazan ke yi wa matayensu, sai dai su rungumi waya a matsayin ƙawar su, abokiyar hirarsu. Tauraruwar labarin ta kasance mace tagari wacce ta yi biyayya ta auri zaɓin iyayenta. Sai dai kash! Sam, ba ta yi dace da mijin da take da muradin samu ba, don bai iya gyara shimfiɗar shi ta aure da soyayya ba, balle lallashi da sauran wasanni da addini ya tanadar don ya zama linzamin da zai wanzar da zaman lafiya a gidan aure. Samun miji mara kula ya sa ta faɗa amfani da sahar sada zumunta ta Facebook, kuma a dalilin mu’amalarta da maza a Facebook ta haɗu da wani saurayin da suka fara soyayya mai narkar da ruhi da gangan jiki. Tun da ta samu muradin ranta sai ta watsar da mijinta da ƴaƴanta ta rungumi waya a matsayin abin da ya fi komai sanya ta nishaɗi, hankalin mijinta ya kai maƙura wajen tashi tun da ya fuskanci canji daga matarsa, ya lura cikin lokaci ƙankani komai ya sauya. Sanadin hakan ya nemo bakin zaren, saboda Tauraruwar labarin mace ce mai ibada da sanin ya kamata.

Shi ma labarin Sanadin Facebook kacokam ɗinsa da gaske ya faru.

Shin ban da rubutu, kina samun lokaci ki karanta littafin wasu marubutan? A halin yanzu wanne littafin ki ke karantawa?

Sosai ma kuwa, ina karatu. A halin yanzu ina karanta littafin Kana Naka…Na Jamila Janafty. Sannan kafin shi na karanta wani littafin na gwanata Bintu Umar Abbale mai suna Ba’aboren Namiji, tabbas wannan labari ya tafi da ruhina. Kamar yadda shi ma wannan sabon da nake karantawa ya ja hankalina sosai, saboda ta kawo wani abu sabo a labarin mai matukar jan hankali.

Da karatun littafi na takarda da aka buga da na waya wanne ya fi miki daɗin karatu?

Gaskiya na fi jin daɗin karanta littafin waya, saboda yadda na saba ta’ammali da waya yanzu.

Shin kina da sha’awar watarana a buga wasu daga cikin littattafanki?

Sosai ina da burin haka, kuma ko ni da kaina na samu dama tabbas zan buga labaraina da kaina idan mai sama Ya yarda, kuma Ya buɗa mini.

Shin ban da rubutu kina da wata ɓoyayyiyar basira da ba kowa ya san ki da ita ba?

E, ina da ita gaskiya. Bayan rubutu ina iya rera waƙa, kuma Allah Ya hore min hikimar sasanta tsakanin mutane, musamman ma’aurata da masoya. Tun ina ƙarama ina da wannan karambanin har ana ce min na cika manyance! A gidanmu ni ce ta kusan ƙarshe, don daga ni sai autan mu, amma ku san kowanne al’amari da ni ake shawara, duk kuwa da wasu a ciki ma sun haife ni. Don haka ina godiya ga Allah akan wannan.

Shin bayan rubutu da waƙa kin taɓa rubuta wasan kwaikwayo na fim? Idan haka ne wanne fim kika rubuta?

Ban taɓa yin rubutun fim ba, amma ina kan hanya, in Sha Allah watarana ina sa ran zan yi.

Zuwa yanzu mene ne babban burinki a harkar rubutu?

Babban burina a duniyar rubutu shi ne Allah Ya ɗaukaka ni, a riƙa labarin cigaban da na samu ta dalilin rubutu. Ina da burin in kai wani matsayi da zan taimaki wasu na ƙasa da ni, kamar yadda wasu ke yi mini kallon madubinsu. Ko dai in kai matsayin da zan taimaka musu da kuɗaɗen da ke cikin asusun ajiyata ko kuma da fikirata, wadda har yanzu bana jin na kai inda na ke so. Amma dai wannan shi ne burina.

Wacce ƙungiyar marubuta kike? Kuma wanne tasiri ƙungiyar ta yi a rubutunki?

A halin yanzu dai ba ni da wata ƙungiya gaskiya, amma na taɓa zama mamba a ƙungiyar Jarumai Writers Association. Babu shakka a wancan lokacin sun taka rawar gani wajen koya mini ƙa’idojin rubutu sosai, sai kungiyar su Pinky, wacce Jidda Washa ta taka rawar gani wajen koya mini wasu muhimman abubuwa. Tabbas, ba zan manta da ƙungiyar Zafafa Writers ba a tarihina.

Yaya harkar rubutun adabi take a Suleja da Jihar Neja bakiɗaya?

A gaskiya ban kai girman da zan iya amsa wannan tambayar ba, saboda ban da daɗe sosai da fara rubutu ba, kuma ban cika shiga cikin mutane ba. Na dai san akwai manyan marubuta sosai a Jihar Neja, maza da mata, masu rubutu da Hausa da kuma Turanci. Musamman kuma idan ana maganar rubutu a Suleja dole a ambaci Hajiya Mairo Muhammad Mudi, wacce ta kasance uwa ce sananniya wajen rubutun Hausa da Turanci. Sannan sai ƙawata Safna Aliyu Jawabi, wacce ita ma fitacciyar marubuciyar onlayin ce. Kwanan nan ma muke magana da ita kan yadda za mu tattara marubutanmu na Jihar Neja, domin samar da wata ƙungiya wacce za mu zauna a karƙashin inuwarta.

Su wane ne iyayen gidanki a harkar rubutun adabi? Kuma su waye ki ka fi kusanci da su a marubuta?

Jibrin Adamu Jibrin Rano shi ne ubangidana a harkan rubutun adabi, yana ƙoƙari sosai wajen ɗora ni akan gwadaben da zai kai ni tudun mun tsira.

Sannan kuma akwai babanmu, Sarkin Mawallafan Arewa, Ado Ahmad Gidan Dabino, bangona ne abin jingina ta. Shi ma ya bani muhimmiyar gudummawa wajen ganin na shiga tsundum cikin marubuta, don ganin an dama da ni. Yana taimakona sosai, kuma ina godiya gare shi.

Ina zumunci da kusan kowa a dangin marubuta, amma na fi samun kusanci da ɗan’uwa, Isma’il Gambo, don yana ɗaya daga cikin aminaina a marubuta. Akwai kuma Aliyu Al’uskun waƙa, akwai Usman Umar Assaƙafi, Safna Aliyu Jawabi, ‘Yar Malam, A’isha Maraɗi, da kuma Fatima Abdul, wacce ita ma ‘yar Nijar ce. Ina da kusanci sosai da waɗannan bayin Allah.

Wanne abu ne ya fi burgeki a mu’amalarki da marubuta, kuma me ki ke ganin ya kamata a gyara?

Son junanmu da mu ke yi, tare da mayar da junanmu tamkar ciki ɗaya muka fito. Marubuta na da tsabar zumunci da mutunta ka. Abin da nake ganin yakamata a gyara shi ne, ƙananan masu tasowa su riƙa girmama na sama da su, su zama masu karɓar gyara, saboda duk wadda ya riga ka kwana dole zai riga ka tashi. Su kuma manyan, idan za su yi wa mutum gyara su yi masa ta siga mai kyau, saboda wasu tamkar suna daƙile ƙarfin gwiwar da wasu sabbi suke da shi ne, saboda kushen da za su yi musu da sunan gyara.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Mai haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa.

Na gode.

Ni ce da godiya.