Ƙungiya ta buƙaci INEC ta soke Abubakar Saddique daga yi wa APC takarar gwamna a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Wata ƙungiya mai zaman kanta, mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubuta wa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ya cire sunan tsohon babban hafsan sojojin sama na ƙasa, Abubakar Saddique daga yi wa Jam’iyyar APC takara a Jihar Bauchi.

Ƙungiyar ta nuna buqatar neman cire sunan Sadique a matsayin ɗan takara na cikin wata takarda da rubuta ta kuma aike wa INEC.

Ƙungiyar ta yi koken cewa ɗan takarar bai gabatar da cikakkun takardunsa ga hukumar zaɓen, kamar yadda doka ta tanada ba.

A cewar ƙungiyar, Air Marshall Abubakar bai sanya wasu muhimman takardunsa waɗanda za su tabbatar da bayanan da ya cike a fom ɗin INEC mai suna EC 9 ba.

Abubakar Sadique a ya riƙe muƙamin babban hafsan sojan sama kafin ritayarsa da kuma shiga siyasa.

Ya zama ɗan takarar Jam’iyyar APC a Bauchin ne bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda-gwani wanda aka gabatar a cikin watan Mayu.