Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata ƙungiya mai suna ‘White Witches and Wizards Association of Nigeria’, ta yi gargaɗi game da yunƙurin kawo cikas a bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban aasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron da suka yi a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Ribas, mai magana da yawun ƙungiyar, Dokta Okhue Oboi, ya yi ikirari gabanin dawowarsa daga hutu a Turai, ƙungiyar ta bai wa zaɓaɓɓen shugaban kariya domin tabbatar da cewa babu wani mummunan abu da ya same shi.
Oboi ya ce, bayan an yi nazari sosai kan al’amuran da ke faruwa a asar nan, taron ya cimma matsaya kan yin kaca-kaca da duk wanda ke shirin kawo cikas a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Ya bayyana fargabar cewa rashin rantsar da Tinubu na iya haifar da tashin hankali ba tare da saninsa ba, wanda ba a tava gani a ƙasar nan ba.
“Mun yi nazari kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan, muna kuma kira ga waɗanda suka yi korafin su baiwa zaman lafiya dama domin neman taimakon kai zai kawo illa ga harkokin siyasa. Babu wani dalilin da zai sa Tinubu ya ji tsoro domin duk kamfen na zage-zage da ake yi masa na raba hankali ne kawai. A halin yanzu muna tsaftacewa da lalata muhallin Abuja inda Tinubu zai yi aiki.
“Abin da Tinubu ke buqata a yanzu shi ne addu’o’in samun lafiya da kuma tsawon rai daga dukkan ’yan Nijeriya domin ya cika alqawarin da ya dauka na sabunta bege domin samun ingantacciyar rayuwa ga kowa,” inji Oboi.
A kan zaven gwamna da za a yi a jihar Kogi, ƙungiyar ta ce, “Mun gana da ‘yan ƙabilar Igala da Ebira da kuma Yarabawa a jihar. Mun sadu da ’yan Igala a Idah, mutanen Ebira a Obehira da Yarabawa a Kabba, muka saurare su.
“Muna ba Dino Melaye shawara ya ganmu idan yana da muradin tabbatar da burinsa na takarar gwamna. Idan ya saurari shawararmu, zai yi dariya domin itatuwa da ruwan jihar Confluence za su zave shi ba tare da la’akari da ko Gwamna Wike ya mara masa baya ba.”
Ƙungiyar ta shawarci ’yan siyasa da su daina amfani da ’yan daba na siyasa wanda a ƙarshe ke haifar da zubar da jini da ƙone-ƙone da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.