Ƙungiyar Ƙabilar Gbagyi ta buƙaci Tinubu ya saka su cikin jerin ministocin sa

Daga SANI AHMAD GIWA

Ƙabilar Gbagyi, wadda ita ce mafi girma a yankin Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya saka su a cikin jerin sunayen ministocin da ke tafe.

Misis Dorothy Nuhu Akenova, wata fitacciyar ‘yar ƙabilar Gbagyi ce ta yi wannan kiran a lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin Nijeriya ranar Juma’a, don roƙon a saka Gbagy a cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu.

A cewarta Ƙungiyar Gbagyi ta buƙaci da kada a yi watsi da ƙabilarsu a lokacin da ake tsara jerin sunayen.

Misis Akenova, wacce ta yi nuni da cewa ƙabilar Gbagyi na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban Nijeriya, ta kuma ce shigar da su cikin jerin ministocin zai iya haɗa alaƙa tsakanin gwamnati da ‘yan asalin ƙasar.

Ta yi imanin cewa shigar da ƙabilar a cikin jerin ministoci zai kawo wani muhimmin ci gaba.

Ƙabilar Gbagyi dai tana wakiltar wani kaso mai tsoka na al’ummar Abuja, kuma ta daɗe tana fafutukar neman ‘yancinta da kuma karɓe ta.

Misis Akenova ta ce al’ummar Gbagyi na da muhimmanci ga ci gaban Nijeriya, don haka akwai buƙatar a ba su wakilci a manyan matakai.

“Babban birnin tarayyar Nijeriya a halin yanzu shi ne mazaunin Gbagyi wanda aka ware don zama wurin idan gwamnati da hukumominta, ba dole ba ne a ce ba za a iya biyan isasshiyar diyya kan irin wannan sadaukarwa.”

Sai dai Misis Dorothy Nuhu Aken’Ova ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi la’akari da wani ɗan ƙabilar Gbagyi a matsayin minista a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya saboda sadaukarwar da suka yi wajen ganin ya yi nasara a zaɓen 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *