Ƙungiyar Ƙasar Sin mai zaman kanta ta bankaɗo laifukan take haƙƙoƙin jama’a da Amurka ta aikata

Daga CMG HAUSA

Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta ƙasar Sin CSHRS, ta fitar da wani rahoton da ya bankaɗo jerin laifuffukan take haƙƙoƙin bil Adama da ƙasar Amurka ta aikata a yankin Gabas ta Tsakiya da kewayensa, wadanda kuma suka yi matuƙar saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Rahoton da ƙungiyar ta fitar a jiya, mai taken “Amurka ta aikata laifuffukan take haƙƙoƙin bil Adama a Gabas ta Tsakiya da kewayensa”, ya mayar da hankali ne kan yadda Amurkar ta keta haƙƙoƙin bil Adama da suka haɗa da ƙaddamar da yaƙe-yaƙe, da yi wa fararen hula kisan kiyashi, da lalata haƙƙoƙin jama’a na rayuwa.

Haɗe da tilasta sauyin rayuwa, da ƙaƙaba takunkumai, da keta haƙƙoƙin al’umma na samun ci gaba da na rayuwa da na kiwon lafiya, waɗanda suka haifar da rikici tsakanin fararen hula da tsananta garƙame mutane, da azabtar da su da take ‘yancin bin addini da mutuncin jama’a.

Rahoton ya jaddada cewa, Amurka ta aikata laifukan yaki da cin zarafi da tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba da yi wa fursunoni gwale-gwale da yin gaban kanta wajen ƙaƙaba takunkumai na ba gaira ba dalili, a yankin Gabas ta Tsakiya da kewayensa.

Ya ƙara da cewa, shaidu sun nuna cewa, Amurka ta yi tsananin keta haƙƙoƙin bil Adama a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran wasu wurare, lamarin da ya haifar da illa da asara ta dindindin ga ƙasashen da al’ummominsu.

A cewar ƙungiyar, yayin da aka bankaɗo dabi’un Amurka na danniya da mugunta da keta, da mummunan tasirin ƙarfinta na siyasa, mutane a faɗin duniya za su kara fahimtar munafurci da yaudara irin na demokuraɗiyyar Amurka da yanayinta na kare haƙƙoƙin jama’a.

Fassarawar Fa’iza Mustapha