Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnati kwana 7 ta kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana bakwai ta kawo ƙarshen wahalar man fetur da ta takardun kuɗi a faɗin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero, ne ya sanar da lokacin da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar ƙungiyar ta ƙasa da ke Abuja, kan matsayin taron ƙungiyar ranar Litinin.

Ya ce, matuƙar ba a iya magance matsalolin ba nan da cikar wa’adin, za su tsunduma yajin aiki.

Shugaban ƙungiyar wanda ya koka da irin mawuyacin halin da wahalhalun suka jefa ’yan Nijeriya, musamman ma ma’aikata ya sa ƙungiyar ba zai yiwu ta ci gaba da yin shiru ba.

“Da farko dai za ku lura da yadda ’yan Nijeriya da dama musamman ma’aikata suke ƙalubalantar yadda suke shan wahala kafin samu kuɗaɗensu daga bankuna. Haka ma matsalar man fetur, inda a wasu wuraren lita yake kai wa har N300, ko ma sama da haka.

“Saboda haka, a kan matsalar ƙarancin kuɗi, muna ba Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da sauran bankuna wa’adin kwana bakwai su magance ta.

“Muddin kuma suka gaza yin haka, za mu buƙaci xaukacin ma’aikata su qaurace wa wuraren ayyukansu, tun da dai ba su da kuɗin zuwa wajen aiki.

“Sannan yin sayayya ma a wajen ’yan kasuwa yana da matuƙar wahala, saboda wasu daga cikinsu ba su da asusun ajiyar bankuna,” in ji shi.

Shugaban na NLC ya kuma zargi wasu Gwamnoni da yin katsa-landan a cikin harkokin ƙungiyar, ta hanyar tursasawa a sanya mutanensu a matsayin Shugabanni a Jihohi.