Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana saka baki da gwamnoni ke yi a batun ƙarancin albashi baya cikin kundin tsarin mulki.
Benson Ujah, shugaban yaɗa labari na ƙungiyar, shiya faɗi haka a yayin tattaunawar sa da gidan talabijin na Arise ranar litinin. Ujah ya jaddada ƙin amincewar su saka baki da gwamnoni sukeyi a kan lamarin ƙarancin albashin.
Yayi bayani yace, hanyar da ake bi domin cimma matsaya a kan mafi ƙarancin albashi shine tattaunawa daga bangare uku, ɓangaren gwamnati, ɓangaren ƙwadago da ɓangaren ma’aikata. Fitar wani ɓangare a wannan gabar cin amana ne.
Ya ƙara da cewa, Najeriya tai ta bin wannan hanyar tun 1961, ƙokarin da gwamnoni sukeyi domin ya zama su ƙadai zasui tattaunawar a mastayin rashin tunani.