Ƙungiyar ɗaliban Zamfara ta ƙaddamar da sabbin shugabanni

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa reshen jihar Zamfara (NUNSZAM) ta zaɓi sabon shugabanta.

Sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa a jihar, Muhammad Bashir Kanto a jawabinsa na karɓar takardar shaidar cin zaɓe, ya yi alƙawarin ɗaukar kowa da kowa.

Bashir Kanto ya ci gaba da cewa, haɗin kai da ci gaba a tsakanin mambobin ƙungiyar a matsayin mafi muhimmanci, yana mai jaddada cewa duk bambance-bambancen cikin gida da ke tsakanin mambobin ƙungiyar za a magance su a ƙarƙashin kulawar sa.

“Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da kowane mamba tare da magance bambance-bambancen siyasar mu ba tare da la’akari da ƙabilanci ko addini a cikin tarayyar don ci gaba ba,” ya ƙara da cewa.

A cewarsa, babu wata ƙungiya ko da za ta ci gaba ba tare da haɗin kan kowace ƙasa ba.

Ya kuma bayyana zaɓen nasu da zaman lafiya da sahihanci, yana mai kira ga membobin da su ba shi goyon baya don tabbatar da jin daɗinsu da kuma ciyar da ƙungiyar zuwa manyan tudu.

A saƙonsa na fatan alheri, Manajan Daraktan/CEO, Zamfara investment Ltd, Hon. Anas Hamisu Lawal ya buqaci sabbin shugabannin ƙungiyar da su mai da hankali kan koyo da karatunsu domin cimma babbar manufarsu.

Ya ƙara da cewa, gidauniyar sa da aka fi sani da Jarumin Gusau Foundation ta ɗauki nauyin ɗaruruwan ɗalibai domin ci gaba da karatunsu a matakin manyan makarantu a Gusau musamman waɗanda ba su da isasshen tallafin kuɗi.

“Shekaru biyar da suka wuce gidauniya ta tana ɗaukar nauyin ɗaruruwan ɗalibai don ci gaba da karatunsu a matakin manyan makarantu a Gusau kuma za mu dore da dan lokaci,” ya ƙara da cewa.

Ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar ɗalibai da su mai da hankali kan adalci ga duk mambobi tare da kare halaccin su a inda ya dace.

“Shugabanci sadaukarwa ce kawai kuma ina roƙon ku da ku nisanci duk wata maslaha ta son zuciya ku riƙe kowa da kowa domin ci gaban ƙungiyar ku.”