Ƙungiyar 13×13 Movement ta raba buhunhunan shinkafa da masara

Daga AMINA YUSUF ALI a KANO

Shugaban ƙungiyar 13×13 Movement na ƙasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya jagoranci raba kayan abinci: Buhunhunan shinkafa da buhunhunan masara wanda ƙungiyar (Buhari For All) ta bai wa ƙungiyar 13×13 Movement kyautar su. Shi kuma shugaban ƙungiyar, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ne ya jagoranci rabawa.

An ba wa kowanne mutum ɗaya buhunan shinkafa uku-uku da buhunhunan masara guda hur-huɗu. Sannan aka ɗora masa kuɗi Naira 20,000 ga kowanne mamba da ke cikin ƙungiyar ta 13×13 Movement.

Mambobin ƙungiyar 13×13 Movement sun yi wa ƙungiyar Buhari For All godiya tare da fatan alheiri a gare su.

Sannan kuma akwai Mallam Sada Idris Kankiya wanda ya kawo wa ƙungiyar 13×13 Movement kyautar babur mai ɗauke da sunan ƙungiyar 13×13 Movement a jikinsa. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kahutu Rarara ya yi wa Mallam Sada Idris Kankiya godiya bisa ƙaunar da yake nuna wa ƙungiyar.