Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a gaggauta sakin ɗalibin da aka tsare kan sukar Aisha Buhari

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta yi kira da a gaggauta sako ɗalibin nan na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu Muhammed, wanda jami’an tsaro suka kama shi don ya soki matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari.

Rahotanni sun ce, jami’an tsaron da ake zargin DSS ne suka damke matashin a ranar 8 ga Nuwamban
2022 biyo bayan wasu kalamai da ya wallafa a shafinsa na Tiwita a kan Aisha Buharin.

Saƙon da Muhammad ya wallafa a wannan rana ya nuna hotunan Aisha a yanayi na can baya da kuma yanzu, inda ya rubuta, “su mama an ci kuɗin talakawa an ƙoshi.”

Cikin wata sanarwa da ta aike wa Daily Nigerian, Ƙungiyar ta yi tir da kama ɗalibin, tare da cewa an kama shi ba tare da wani bayani ba sannan kuma an gallaza masa azaba.

A cewarta, “Tun bayan da aka kama shi, danginsa ko lauyansa babu wanda ya samu ganin sa.

“Zargi mai ƙarfi ya nuna Aminu na hannun jami’an tsaron Nijeriya a wani yankin Abuja da ba a sani ba.

“Ƙungiyar Amnesty International na kira ga hukumomi da a sako wanda aka kama ɗin ba bisa ƙa’ida ba, sannan a tabbata da adalci kan azabtar da shi da aka yi,” inji Ƙungiyar.