Ƙungiyar Direbobin Tifa ta rantsar da sabbin shugabaninta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Direbobin Tifa ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta rantsar da sabbin shugabanin rassan ƙungiyar da ke Kano.

Ƙungiyar dai ta gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabanin rassan guda 196 da ya gudana a sakatariyar ƙungiyar da ke Kano a Lahadin da ta gabata.

Da ya ke jawabi shugaban ƙungiyar ’yan tifa na jihar nan Mamunu Ibrahim Takai, ya buƙaci sabbin shugabanin rassan da su kasance masu kwatanta adalci wajen sauke nauyin da ke kansu.

Shi ma a jawabinsa, shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa na ƙasa reshen Kano da Jigawa da Bauchi Maude Nasir, ya ce, suna da kyakkyawar alaƙa da direbobin tifa a jihar nan sabanin yadda ake samun ƙananan matsaloli daga wasu masu tsamo yashi.

Shi ma da ya halarci taron, Wazirin Garin Malam, Abubakar Rabo Abdulkarim, ya yabawa uwar ƙungiyar ta direbobin Tifar bisa yadda suke tallafawa marasa galihu da ke cikin su da kuma yara marayu da iyayen su direbobi suka rasu.

Sannan malam Rabo ya buƙaci direbobin da su cigaba da bin doka da oda yayin da suke gudanar da ayyukan su na ɗibar yashi da kuma tuƙi a cikin gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *