Ƙungiyar GOBA na matuƙar tallafa wa harkar ilimi – Malam Gali Bala

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Daraktan makarantar sakandare ta Gwale kuma shugaban Makarantar, Malam Gali Bala Muktar ya yaba wa ƙungiyar tsofafin ɗalibai ta GOBA kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen tallafin ilimi kamar yadda gwamnati da sauran al’umma masu shi ilimi a kowa ne mataki suke so a yi.

Shugaban Makarantar Gwale ya bayyana haka a lokacin taron ƙungiyar ta GOBA Aji na 1991 da akayi a ranar Lahadi da ta gabatar a harabar makarantar Gwale a ƙaramar hukumar Gwale da ke Kanon dabo Nijeriya.

Malam Gali ya qara da cewa, in aka dubi yadda waɗannan tsofafin ɗalibai tun daga kan uwar ƙungiyar ta ƙasa ta ke bayarwa zuwa kan ɗaiɗaikun tsofafin ɗaliban Gwale abun yabo ne kuma abun a yi koyi ne da su ne kan wannan lamari na tallafawa ilimi ta hanya gine gine a makarantar don sabanta da Kujeru da Tebura da dai sauran kayan aiki na koyo da koyar da wannan abun farin ciki ne da ɗaukacin al’umma ta Gari.

Shi kuwa Alhaji Abdullahi Muhammad Gaya tsowan ɗalibi a makarantar Gwale na ƙungiyar GOBA Aji na 1991 wanda kuma shi ne ya assasa wannan ƙungiya ta kafar yaɗa labarai na zamani ta hanyar waya kamar yadda bincike ya nu na mana, Gaya farin cikinsa yayi kan wannan taro na ƙungiyar wanda aka samo haɗuwa don sadar da zumunci da taimakon juna da ita kanta Makarantar hakan ta faranta masa rai.

Jawabai gada shugabanin Goba aji na 1991 sun nuna farin cikinsu ne kan yadda wannan ƙungiya ya ta samo nasarar ba da gudunmawa ga Makaranta ta fuskar kujeru da gyaran masallaci da dai sauransu.

Daga cikin mambobi na Goba aji na 91 akwai Malam Musubahu Yakasai ɗaya daga cikin ma’aikatan ma’aikatar yaɗa labarai ta Kano Masani ne na aikin yaɗa labarai mai qoqari da iya hurɗa da jama’a da dattako wanda kuma shi ne jami’in hulɗa da Jama’a mai dattako wanda kuma shi ne jami’in hurɗa da jami’in Goba 91 sai kuma Malam Munzali Hauwasa na Rido Kano. Barista Badaru Suleman shi ne shugaban Goba Aji na 1991 a kano.