
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar goyon bayan Shugaba Tinubu ta (NTCA), ta naɗa toshon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin babban tauraro a tafiyarsu.
NTCA, wadda ke da mambobi a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje, ta na ƙoƙari ne wajen ɗaukaka ayyukan Shugaba Bola Tinubu da ke ƙunshe da inganta harkokin tattalin arziƙi da siyasa a ƙasar.
Waɗanda suka gabatar naɗin ga tsohon gwamnan sun haɗa da Kodinetan ƙungiyar, Hon. Henry Nwabueze da Shugaban Wayar da kai, Dakta Haruna Madisca.
A sanarwar da ta fitar, ta ce ta naɗa Yahaya Bello, wanda aka fi sani da ‘The White Lion’ a matsayin babban tauraron Shugaba Tinubu daga ƙungiyar.
Ƙungiyar dai ta na fafutukar dawo da martabar Nijeriya ne ta hanyar haɗa kan baki ɗaya jihohin ƙasar har da Abuja, inda ta yi alwashin mara wa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.