Ƙungiyar GSK ta kashe miliyan N50 a cibiyoyin kiwon lafiya na Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Wata ƙungiya mai rajin kare lafiyar ƙananan yara tare da haɗin gwiwar GSK ƙarkashin shirin yaƙi da cutar nimoniya sun samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya da magunguna wanda kuɗin su ya kai aƙalla naira miliyan 50 a cibiyoyin lafiya guda 35 a Jihar Jigawa.

Shugaban shirin yaƙi da cutar nimoniya, Dakta Adamu Isah ya bayyana hakan a lokacin da ya ke miƙa kayayyakin tallafin ga Gwamnatin Jihar jigawa wanda aka gudanar a ofishin ƙungiyar ceto ƙananan yara da ke Dutse.

A cewarsa, sun samar da kayayyakin tallafin ne bayan nazarin da suka yi sakamakon duba da ƙungiyar ta yi akan yadda harkokin kiwon lafiya ke gudana a qaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa.

Ya kuma ƙara da cewa, manufar hakan ita ce domin a cike giɓin da aka samu a yayin horarwar da ƙungiyar ‘save the children’ ta gudanar akan yadda za a daƙile kamuwa da kuma yaɗuwar cututtuka wanda aka gudanar a cibiyoyin lafiya.

Dakta Adamu Isah ya ƙara da cewa, tallafin zai ƙara inganta hoɓɓasar da gwamnatin Jihar Jigawa ta ke yi wajen bunƙasa harkokin samar da lafiya a faɗin Jihar.

Ya ƙara da cewa, akwai buƙatar cibiyoyin lafiya su kasance a cikin shiri domin samar da ingantaccen kulawa ga masu jinya musamman yaran da suke fama da cutar nimoniya da sauran cututtukan da ke addabarsu.

Shugaban shirin yaƙi da nimoniyar ya ce kwalliya ba zata biya kuɗin sabulu ba, har sai an samar da nagartattun kayayyakin aikin da za a yi amfani da su wajen ceto rayukan al’umma.

Da yake karɓar tallafin a madadin gwamnatin Jihar, babban sakatare na ma’aikatar lafiya kuma muƙaddashin kwamishinan lafiya na Jihar Jigawa, Dakta Salisu Mu’azu ya ce nimoniya yana haifar da mace macen da dama musamman a ƙananan yara.