Ƙungiyar haɗin kan Fulani ta ƙaddamar da sabbin shugabanninta a Legas

Daga DAUDA USMAN e Legas

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne ƙungiyar Haɗin Kan Fulani ta Nijeriya, wadda aka fi sani da Kautal Hore ta gudanar da bikin ƙaddamar da shugabanninta na Jihar Legas da ƙewayenta gabaɗaya.

Taron ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar a Legas ya samu halartar shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Bello Badejo da tawagarsa da Sarkin Fulanin Jihar Legas, Dakta Alhaji mohammed Abubakar Bambado na biyu wanda ya samu wakilcin Mai Martaba Sarkin Hausawan Unguwar Ojoromi Ifeledun a Jegunle, Alhaji Adamu Nebi da shugabannin ƙungiyar na jihohi shida da ke yammacin Nijeriya, waɗanda suka ƙunshi Legas, Ogun, Oyo, Osun, Ikikiti da Ondo da na waɗansu  jihohi na arewacin Nijeriya da sauran al’ummar Hausawan jihar Legas gabaɗaya.

Taron ya gudana ne a harabar ofishin ƙungiyar ta Kautal Hore da ke cikin babbar mayankar shanu ta abbatuwa unguwar Okoba Agege ta ƙaramar Hukumar Ijaye Okokoro da ke cikin garin Legas.

Uban taro, sarkin Fulanin abbatuwa Alhaji Bello Dammubaffa mai masaukin baƙi Alhaji Abdullahi Lelega da sauran makamantansu tun da farkon buɗe taro da addu’a, shugaban ƙungiyar ta Kautal Hore na ƙasa Alhaji Bello badejo ya ba da izini aka fara ƙaddamar da Alhaji Bello Mohammed Liman a matsayin shugaban ƙungiyar na jihar Legas gaba ɗaya sannan aka ƙaddamar da mataimakinsa na ɗaya Magaji Bello ƙarshe aka ƙaddamar da mataimakinsa na biyu Ahmed Suleman Shanono tare da ba su satifiket wato takardar shaidar cewa an ba su wannan muƙami kuma su kasance sune masu ruwa da tsaki a wajan gudanar da harkokin ƙungiyar a Legas.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Bello badejo a huɗubarsa ga sababbin shugabannin ƙungiyar ta Kautel Hore a wajen taron ƙaddamar war ya jawo hankulan su ne su zama wakilan ƙungiyar nagari kuma su zama masu ƙoƙari a wajen haɗa kawunan mambobin ƙungiyar sannan kuma su tsaya tsayin daka a wajan nemo wa ƙungiyar mutunci tare da kawo cigabanta a Legas da kewayenta gabaɗaya.

Ya cigaba da yin kira ga filanin Nijeriya da su zauna lafiya da kowa kuma su guji aro halayen da ba nasu ba su riƙa amfani da su a wajen gudanar da harkokin rayuwar su domin gyara tarbiyyar Fulani tare da dawo da mar tabar fillanci a Nijeriya gabaɗaya.

Sabon shugaban ƙungiyar ta Kautal Hore a Legas Alhaji Bello Mohammed Liman ya yi jawabin godiya ga shugabannin ƙungiyar na ƙasa da wakilanta na jihohi da dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin ƙungiyar.

Ya ce, yana yi wa kowa fatan alheri na komawar su gidajen su lafiya sauran jawaban da suka gudana a wajan taron waɗanda suka fito daga bakunan sauran al’umma waɗanda suka sa mu yin tsokaci awajan taron dukkan jawaban su sun karkata ne a wajen taya sababbin shugabannin ƙungiyar murna tare da kiraye-kiraye ga al’ummar filani da su zauna lafiya da kowa tare da haɗa kawunan junansu a Nijeriya gaba ɗaya