Ƙungiyar Hisbah a Katsina ta yi taron shekara

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Hisba ta Ƙasa, reshen Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Muhammad Rabiu Garba, ta gudanar da taron shugabanni karo na farko.

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata takardar da aka fiddo bayan taro da sakataren ƙungiyar ACH. Muhammad Aminu Bello ya sawa hannu ya raba wa manema labarai a jihar.

A cewar sanarwar taron ya samu halartar kananan hukumomi talatin cikin talatin da huɗu da ke akwai a jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, kwamandojin waɗannan ƙananan hukumomi talatin sun jaddada mubaya’a ga kwamanda na Jiha CH. Muhammad Rabi’u Garba.

Taron ya samu halarcin manyan baƙi da suka haɗa da Wakilin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Durbin Katsina, Wakilin Daraktan DSS na JIha, Kwamandan Vigilate na Jiha, Wakilin DPO da Barr. Haj Fatima muhammad jibo Esq, da dai sauransu.

Sannan ƙungiyar ta Hisbah ta ce akwai takardu na ɓatanci da ke yawo akan wai an kori wasu ’yan Hisbah guda takwas, waɗanda waɗannan takardu ba halattatattu ba ne, tsohon shugaba da ya sauka da kanshi ne ya fitar da su domin ɓatanci da tada fitina.

Kuma dukkan waɗanda ake yada cewa wai an kore su sunanan a halattattun yan Hisbah kuma official na jiha, kowa da miqaminsa, bugu da ƙari kuma duk sun halarci taron na ranar lahadi cikin cikakkun uniform ɗinsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a madadin shugaban na jihar Katsina ƙungiyar na Mika saƙon taya murna ga sabon kwamandan Hisbah na Jihar Kano sheikh Aminu Daurawa bisa wannan muƙami da ya ƙara samu karo na biyu.

Kazalika rundunar hisba ta jihar Katsina takara bayyana addu’o’in ta ga sheikh Aminu Daurawa fatan Allah yayi masa jagoranci tare da gudanar da aikin cikin nasara.

Manyan bakin sun tabbatar da goyon bayansu ga Hisbar Jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin CH. Muhammad Rabi’u Garba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *