Ƙungiyar Ibo ta yi Allah wadai da kashe sojoji a Anambara

Manhaja logo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata ƙungiya ’yan ƙabilar Ibo ta IPN, ta yi Allah-wadai da harin kwanton vauna da aka yi wa wasu sojoji da ke sintiri a garin Umunze da ke ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra.

Wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Anayo Mbakwe ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana lamarin a matsayin wani bala’i, dabbanci da rashin sanin yakamata.

Mbakwe ya ce, “mutanen kudu maso gabas an san su da nuna ƙauna, maraba da karvar baƙi. Abubuwan da suka faru, musamman a Anambara babban abin damuwa ne.

Ƙungiyar ta tuna damuwarta kan yunƙurin kashe Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah a kwanakin baya a Nkwo Enugwu-Ukwu a ƙaramar hukumar Njikoka.

Kuma Mbakwe ya yi imanin cewa waɗannan abubuwa guda biyu marasa daɗi suna da kamanceceniya kuma suna firgitarwa ga al’ummar qasa gaba ɗaya da kuma musamman a ƙasar Ibo.

Ya ce, “Kisa na kowane irin nau’i, na siyasa, tayar da hankali ko na bazata aikin ta’addanci ne kuma bai kamata a yarda da shi ba.”

Don haka ya yi kira ga jami’an tsaro da su kamo masu laifin tare miƙa su ga koliya.

Mbakwe ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su shawo kan matsalar kashe-kashen da ake ta yi a Anambara, musamman ganin zaɓen 2023 da ke gabatowa.

Yayin da suke yabawa rundunar sojin Nkjeriya bisa wasu gaggarumin cigaba da aka samu a yankin da ma faɗin ƙasar, ’yan ƙabilar Ibo na Nkjeriya sun ce kamata ya yi babban hafsan sojin ya maida hankali ga Anambara.

Ya ce, bai kamata sojoji su yi aasa a gwiwa ba kan nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, yana mai cewa tuni aka daƙile yawancin hanyoyin da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen yin varna.

Don haka Mbakwe ya buƙaci rundunar da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen maido da doka da oda da sauran hukumomin tsaro kamar yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, babban kwamandan askarawan ƙasa ya umarta.

Ya ce, duk da haka, ‘yan ƙabilar Ibo suna alfahari da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi a yankin.

Ƙungiyar ta Ibo, ta yi kira ga Ndigbo da kada su naze hannayensu su kalli irin wannan muguwar ɗabi’ar ta ƙara ta’azzara.

Ya ƙara da cewa, masu aikata laifuka a cikin al’umma, walau ’yan asali ne ko kuma baƙi, a kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *