Ƙungiyar IDDEP ta ba da tallafin yi wa yara kaciya a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Aƙalla yara 450 ne suka samu tallafin yi musu kaciya kyauta daga Ƙungiyar tallafa wa mabuƙata ta IDDEP, wato ‘Insana Deger Veren Dernekler’ tare da kulawar Cibiyar bincike da yaɗa ilimi ta Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, wato ‘Sheikh Muhammad Nasiru Kabara Research Center’. Da Malam Askiya Nasiru Kabara ya ke Jagoranta.

Wannan dai shi ne Karo na shida da ƙungiyar ta saba yin wannan aiki na kaciyar yara a duk shekara, wanda Kuma a wannan shekarar aka samu ƙarin yaran da a ke yi wa daga 300 zuwa 450.

Shugabar ƙungiyar ɓangaren mata da yara, Balaraba Kabir Madaki a lokacin da take bayani a Kan yadda ayyukan su ke gudana ta bayyana cewa, “wannan aikin na yi wa yara kaciya mun Kai shekaru shida muna gudanar da shi a duk shekara, wanda a baya muna yi wa yara 300 ne, to amma a wannan shekara mun ƙara zuwa 450, Wanda a yanzu muna cikin rana ta uku kuma ta ƙarshe, domin mun fara ne a ranar Asabar 25 ga watan Disamba muka sai 26 da kuma yau 27 rana ta ƙarshe, Kuma kullum muna yi wa yara 150 ne yau ce ranar ƙarshe ta aikin a wannan shekarar”.

Dangane da tsarin da su ke bi wajen haɗa yaran domin yi musu kaciyar kuwa cewa ta yi tsarin da mu ke bi, mu Kan sanar da iyayen yara ne cewar za mu fara ɗaukar yara da za a yi musu kaciya, duk wanda ya ke da yaron da za a yi masa sai a turo da sunayen yara, don a shigar da su, Kuma idan mun tattara sunan sai mu saka lokaci kamar yadda ka gani ana yi yanzu. Kafin ma a yi musu sai an saka musu ƙaramar riga don ta yi daidai da masu kaciya yadda ba za ta rinƙa taɓa musu wajen Kaciyar ba.

Kuma idan an kammala a Kan tara iyayen yaran likitoci su yi musu bayani yadda za su kula da yaran na su, sannan Kuma akwai magani da a ke, kuwanne guda shida na kariya da cututtuka, sai Kuma Shanu da a ke yankawa ana raba wa kowanne yaro da aka yi masa, sai Kuma ɗan kuɗin abin hawa da mu ke bayarwa saboda wasu ma ba su da kuɗin da za su koma gida saboda halin rayuwa da a ke ciki.

Da muka yi ma ta tambaya a game da nasarorin da su ke samu kuwa cewa ta yi, to gaskiya nasarori kullum a cikin su a ke musamman ha]in kan da jama’a su ke ba mu musamman ta ɓangaren shugabanni da iyayen yara. Sai dai duk da haka ba a rasa wasu matsaloli da su ke tasowa, don wasu ma sai ka ga a lokacin da mu ke tsaka da aikin, sai a lokacin su ke kawo yaran su Kuma su ce a lokacin su ke so a yi musu  to ka ga wannan abin ya Kan ba mu ‘yar matsala saboda tsawon lokacin da muka yi muna sanarwa, sai mun shiga aikin ko muna rana ta ƙarshe kamar yau wasu za su zo da yaran su.

Daga ƙarshe ta yi Kira ga dukkan ɓangarori na Jama’a da su zo a yi wannan aikin da su ko Kuma su yi a ɗaiɗaikun su domin taimaka wa mabuƙata, saboda akwai Mutane masu yawa da ba su da Halin da za su yi wa yaran na su kaciya, don haka idan Jama’a suka bayar da ta su gudummawar to za a samu sauki musamman a wannan rayuwar da a ke ciki a yanzu.