Ƙungiyoyin Islama sun shiga sahun masu nazari kan gyaran haraji

Daga BELLO A. BABAJI

Wata tawagar haɗaka ta ƙungiyoyin addinin Islama ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar haɗin kan al’ummar musulmi (IFUU) ta shirya tattaunawa game da ƙudirorin gyaran haraji da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙirƙiro.

A ranar Laraba ne za a gudanar da zaman inda tawagar ta ce tsarin gwamnati na neman kwaskwarima wa haraji abu ne da ke da buƙatar neman shawarwari daga masu-ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi da kuma al’umma kafin zartar da shi a matsayin doka.

A ranar 3 ga watan Satumba ne Tinubu ya miƙa ƙudirorin neman gyaran haraji ga Majalisa domin dubawa.

Cikin wani jawabi da ke ɗauke da sanya hannayen Shugaba, Malam Awwal Muhammad da Sakatare, Shaikh Akanbi Rashidi Bolaji, IFUU ta nuna damuwa kan yadda gwamnonin Arewa da Majalisar Tattali (NEC) suka ƙi amincewa da su tare da kira da a janye su.

Mambobin ƙungiyoyin Islaman za su tattauna ne kan yadda hakan ya shafi tattali da kuma amfaninsa ga al’ummar Musulmi a Nijeriya don cimma matsayarsu.

Gwamnonin dai sun koka ne kan yadda tsarin harajin VAT ya ci karo da abin da aka gina Arewa da wasu yankuna akai na tsarin gudanar da al’umma a shiyyar.

Ƙudirorin harajin sun ƙunshi sanya kaso ga kowane ɓangare da al’umma ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum a kai.