Ƙungiyar KAFIGAN ta jajenta rasuwar fitaccen Jarumi Baba Karƙuzu

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƴan finafinan Kannywood, wato KAFIGAN, ta yi alhini tare da jajenta rasuwar tsohon ɗan wasan fim ɗin Hausa, Malam Abdullahi Shu’aibu da aka fi sani da Karƙuzu Na-Bodara.

Karƙuzu ɗaya ne daga cikin taurarin finafinan Hausa da suka jima suna nishaɗantar da al’umma musamman a ƙasar Hausa, wanda mutuwarsa ta haifar da babban giɓi ga masana’antar, inda zai yi wahala a maye gurbin da ya bari.

Darakta-Janar na KAFIGAN, Hon. Adamu Bello ya bayyana jimaminsa game da babban rashin tare da masa addu’ar fatan samun rahamar Allah (SWT).

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalansa da masana’antar Kannywood da ƴaƴanta gami da ɗaukacin al’ummar Hausa.

An gudanar da jana’izarsa ne a gidansa dake garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato a safiyar ranar Laraba.