Ƙungiyar kare ’yancin jama’a ta yi zargin mulkin ƙabilanci a Jami’ar NOUN

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar kare ’yancin jama’a ta buƙaci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shiga tsakanin ma’aikatan Jami’ar NOUN ta Abuja da jagororinta.

Ƙungiyar ta yi ƙorafin cewar ba a yi wa ’ya’yan ƙungiyar adalci, kuma ana yi wa ma’aikatan babakere da rashin adalci a makarantar.

Ƙungiyar ta ce, tana zargin akwai wata maƙarƙashiya da da ake yi wa wasu wajen naɗa muƙamai da suke jagorantar Hukumar Makarantun na NOUN a matakin hediƙwatar ta zargi ƙungiyar da naɗa wasu da basu cancanta ba a manyan muƙamai maimakon ayi daidai kamar yadda dokar Gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen ɗaukar ma’aikatan Gwamnatin tarayya.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin ambasada Sulaiman Idris Uwaisu, Babban sakataren gaba ɗaya na ƙungiyar ta ƙasa wadda yasa hannu aka rabawa manema labarai cikin makon nan.

Kamar yadda kowa ya sani NOUN tana ɗaya daga cikin manyan Jami’o’in Nijeriya da Gwamnatin Nijeriya ta ƙirƙira a shekarun baya da nufin taimaka wa mutane su mallaki kwalin karatu, kuma ita ce jami’a ta farko a faɗin Afirika da ake karatu na hanyar sadarwa.

Uwaisu ya qara da cewa, duk da irin wannan abin alfahari da gwamnatin tarayya ta yi yana neman lalacewa saboda wasu na neman mamaye komai ta fuskar jagorancin ƙungiyar makarantun na NOUN da ke faɗin Nijeriya.

Sakataran ƙungiyar ya ci gaba da cewa, dukkan ɗaukacin muƙaman da yakamata a yi raba daidai tsakanin mabiya addinan ƙasarnan guda biyu ba a yi hakan ba, maimakon hakan kiristoci sun mamaye gaba ɗaya wadda suka haɗa da muqamin shugaban gudanarwa na makarantun na NOUN da Farfeso Peter Oke Bukola yake Kai haka kujerar mataimakin Cansala kiristane.

Yayin da sauran kujerun da aka mamaye suka haɗa da kujerar DVC da kujerar gudanarwa na ‘Admin’ da kujerar maga takardar makarantar da kujerar Bursa hatta ta shugaban ɗakin karatu, dukkansu kiristoci ne babu musulmi ko ɗaya.

Saboda haka ya buƙaci Gwamnatin tarayya ta gaggauta duba matsalar domin shawo kan matsalar cikin gaggawa, ya ƙara da cewa, wanna matsalar ba abu ne da za a sanya ido a yi shuru ba, ya zama dole hukuma ta binciki lamarin domin kawo ƙarshen matsalar jami’ar da ke Babban Birnin Tarayya.

Kamar yadda Uwaisu ya ce, “dukkanmu ’yan Nijeriya ne, muna da ’yanci kamar kowa, don haka bai kamata a fifita wani ɓangare ba akan wani ɓangare ba kasancewar dukkanmu ’yan ƙasa ne saboda haka ’yancinmu ɗaya ne ba tare da an duba ɓangaranci ko addini ba”.

Uwaisu ya nuna damuwarsa akan nuna ƙabilanci da ake nuna wa musulmi a ɓangaran madafun iko wajen jagorancin makarantar da ke Birnin Tarayyar Nijeriya, saboda haka ya buƙaci gwamnatin tarayya da duba matsalarsu cikin gaggawa domin shawokan lamarin cikin hanzari.

Da yake kare Hukumar ta NOUN, wani Mai magana da yawunta, Mista Bayo wadda yaƙi fadar muƙaminsa ya ce, wadda ya raba ƙorafin ga ’yan jarida bai masu adalci ba domin bai basu kwafiba kuma ba haka yakamata a ce yayi ba, kamata yayi ya kai wa lauya kwafi shikuma lauyan ya sami Hukumar NOUN da ƙorafin.

Bayo ya ce, su ba za su yi magana da manema labarai ba matuƙar babu wadda ya ba su ƙorafin a rubuce kamar yadda yadda shaida wa wakilinmu ta wayar salula.