Ƙungiyar ma’aiktan aikin gona ta Kano ta zaɓi shugabannin riƙon ƙwarya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan aikin gona ta ƙasa reshen Jihar Kano, wato Nigerian Union of Agriculture and Allied Employees, (UNAAE)
ta ƙaddamar da shugabannin shiyyoyin ƙungiyar da za su jagoranci yankinsu na wata uku.

A jawabinsa, manajan darakta na hukumar aikin gona na Jihar Kano KNARDA Dr. Faruku Kurawa wanda daraktan istanshan na KNARDA Gambo Isa Garko ya wakilta, ya yaba da shugabannin riƙon na ƙungiyar reshen Jihar Kano da suka zaɓo waɗannan jajirtattun masu riƙon kwaryar.

Ya Kuma ja hankalin waɗanda aka naɗa da su fahimci cewa riƙon ƙwarya aka ba su ba na dindin ba, su yi ƙoƙari idan akwai wasu kurakurai da aka yi a baya to su gyara su ta yadda zai zama idan zaɓaɓɓun shugabannin su ka zo za su samu sauƙin tafiyar da Ƙungiyar.

Tunda farko a jawabinsa, kwamared Zaharadden Abdullahi Yakasai ya bayyana rantsar da kiyatekar a matsayin babbar nasara.

Ya ƙara da cewa cewa ” Mun rantsar da shugabann rassan da muke so su yi shi ne su bi hanya sahihiya don gudanar da zaɓe a nan gaba, don ciyar da su gaba da kuma kyautata harkar aiki”

Mun ba su dama ga duk wanda ya ke da sha’awar ya shubabanci ma’aikatarsa ya fito ya tsaya mutane su zaɓe shi.

“A cikin membobin ƙungiya fiye da mutum dubu aka zaɓo su aka ba su wannan muƙami, don haka nake kira a garesu da su yi aldalci kuma su riƙe amana su ji tsoron Allah” cewar kwamared Abdul’aziz

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, shugabannin da aka rantsar za su yi wata uku suna jan ragamar Ƙungiyar manoma ta (UNAAE), sannan
tana da membobin sama da 3,000 a cikin rassan na Jihar Kano baki ɗaya