Ƙungiyar manoma albasa ta horar da mata dabarun sarrafa albasa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Horarwar dai a cewar shugaban ƙungiyar masu noma da kasuwancin albasar na ƙasa, Aliyu Mai Tasamu Isa, na da manufar koyar da matan karkara yadda za su riƙa sarrafa albasa ta hanyar busar da ita, domin rage yawan asarar da ake yi na albasar a lokuta da dama.

“Wannan shirin an shirya shi ne saboda a koyar da mata yadda za su yi ta sarrafa albasa zuwa abubuwa daban-daban, kana da masaniya ana sarrafa albasa zuwa tsakin albasa, akwai gabun albasa idan ya bushe, ana iya sarrafa albasa a yi lemo, ana amfani da albasa a yi alewa, cincin, biskits kai abubuwa da yawa,” inji shi.

Da wannan hararwar dai a cewar shugaban zai taimaka wa matan wajen sarrafa albasar da ma dogaro da kansu.

Ya ƙara da cewa, “sai kaga cewa matanmu ba su da wannan ƙwarewar na mayar da albasa zuwa abubuwa daban-daban sai mu ka samo mata ƙwararru suka zo suka koyar da su ta inda za su iya sarrafa albasar, yadda suma za su ɗauke shi a matsayin sana’a suna ɗaukar albasa suna sayarwa, kuma wannan shirin mun yi shi ne tare da wata ƙungiya da ba ta gwamnati ba Two scale, da kuma kamfanin Taste Food Limited sun yi haɗaka ne suka yi wannan kuma an kashe kusan aƙalla naira miliyan ɗaya da rabi wajen aiwatar da shirin nan”.

“Kafin ƙaddamar da shirin said a wannan ƙungiya suka ce sai mun tanadi N750,000 watau rabin abin da muke buƙata, to cikin ikon Allah da muka faɗa wa jama’a sai aka samu N800,000 to sai su suka ƙara mana da N750,000, to shi ne aka saye injinan da ake busar da albasa ka gane su can guda uku, mai amfani da hasken rana saboda ƙauyuka ko cikin abin nan ma babu wuta ballantana ƙauyuka, da kuma wani injin da suke amfani dashi na yanka albasa,” ini shi.

Ƙananan hukumomi uku ne dai daga cikin ƙananan hukumomin mulki 23 da ke akwai a jihar Sokoto suka soma amfana da wannan shirin na sarrafa albasa zuwa busassa.

Ya ci gaba da cewa, “yanzu dai mun zaɓo mata daga ƙananan hukumomi guda uku, akwai garin Cimola ƙaramar hukumar mulki ta Gwadabawa, akwai a Wurno sai kuma Dange Shuni a ƙauyen Shuni, kuma wannan horarwa mun bashe ta ne ga jagororin su, kasantuwar a ƙungiyarsu matan suna da yawa suna kai 50 amma yanzu da za a yi wannan taron sai aka zaƙulo  shuwagabannin mata su huɗu-huɗu wani wuri uku ga ko wacce ƙungiya kamar ita shugaba da sakatariya da kuma ma’aji, aka ba su horarwa su ma ana tunanin in suka koma ƙauye su horar da saura dalla-dalla kan wannan shirin”.

Su ma wasu daga cikin waɗanda suka samu horon sun shaida wa Manhaja yadda horon zai tallafa wa rayuwarsu, kamar irin su Malama Aisha Isah da ta fito daga ƙaramar hukumar mulkin Wurno.

Ta ce, “gaskiya Alhamdulillahi ni da ‘yan ƙungiyata gaskiya mu kanmu haɗe ya ke, kuma lallai babu ila shakka ni ƙungiyata tana da dama, don akwai ta shinkafa akwai ta albasa muna nomanta kuma muna sarrafa ta, dan haka duk abin da aka koyar da mu sai dai mu ce Alhamdulillah, ni na riga na karance shi daga zuciyata zan zo in horar da ’yan ƙungiyata manyansu da waɗanda ya ke suna zaune cikin dakunansu, ka ga mun samu sana’a sannan kuma sun samu abin da za su kama tallafa wa mazansu.

Ita ma dai malama Zalihatu Umar da ta fito daga ƙaramar hukumar mulkin Dange-shuni ta bayyana cewa, ba makawa wannan shirin zai tallafi rayuwarsu matan karkara wajen raba su da zaman kashe wanda.

“Gaskiya muna sa ran abin zai ɗaukaka mata sosai kuma mu za mu ci gaba ga wanga abu Allah ya sanya wannan abin ya zama mana alkhairi,” inji ɗaya daga cikin waɗanda aka horar ɗin.

Mai horarwar ya ce, “eh gaskiya Alhamdulillahi sun yi ƙoƙari, gaskiya sun nuna sha’awa kuma sun yi ƙoƙari da horar ɗin da muka yi musu kuma sun gamsu in sha Allahu.”

Ɗaya daga cikin matan da suka bayar da horon ta bayyana cewa, ba makawa da irin kwazon da ɗaliban na su suka nunar tofa kwalliya za ta kai da biyan kuɗin sabulu.

Ta ce, “eh Insha Allah za su iya samar da kyakkyawan sakamako saboda sun nuna suna so, ka ga mutum yana son abu zai sa kai ya koya, kuma sun sa kai wajen horarwar cikin farin ciki da annashawa, kuma Alhamdulillahi.”