Ƙungiyar Mar’atissaliha ta Afirka ta karrama masu yi wa addini da marayu hidima

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato

Ƙungiyar Mar’atissaliha ta Afirka ta ba da wannan karrama Mai Martaba Sarkin Kabbin Argungu da Mai Girma Ajiyan Kabbi Babba Alhaji Yusuf Abubakar Argungu da lambobin yabo ne sakamakon hidimar da suke yi ga rayuwar marayu da addinin Musulunci.

ƙungiyar wacce a turance ake kira da Mar’atissaliha ‘Widows And Orphans Initiatiɓes for Africa’ tana mayar da hankali ne wajen tallafawa marayu da uwayensu mata, da ‘yam mata, da sauran mabuƙata a ƙasar nan da wasu ƙasashen Afirka, ƙarƙashin jagorancin Malama Khadeeja Mar’atissaliha wadda ta kasance ƙwararriya a fannin gyaran zamantakewar aure da kula da lafiyar ma’aurata da kuma koya wa sababbin ma’aurata sirrin zaman aure.

A yayin wani taro da Shugabar ƙungiyar ta ƙasa da takwararta ta reshen Argungu, Hajiya Mariya Muhammad Mera suka gudanar a fadar Mai Martaba Sarkin Kabbin Argungu, ƙungiyar ta yabawa ƙoƙarin da Mai Martaba da Ajiyan Kabbi Babba da wasu fitattun mutane a masarautar Kabbin Argungu, da suke nuna jajircewa wajen taimakawa marayu da mabuƙata, da ke rayuwa cikin wani mawuyacin hali.

Sun kuma ƙara kira ga sauran masu faɗa a ji da masu riƙe da muƙaman siyasa da rawunan gargajiya a masarautar Kabbi, Jihar Sakkwato da sauran sassan ƙasar nan, da su yi koyi da halayen waɗannan manyan ƙasa suke yi, don tausayawa da nuna jin ƙai ga raunana a cikin jama’ar su.

Daga bisani an miƙa shaidar yabo da karramawa ga Mai Martaba da Ajiyan Kabi Babba, bisa ga gudunmawar da suke bayarwa wajen farantawa marayu da mata iyayen marayu a rayuwarsu.