Ƙungiyar matasa ta nemi haɗin kan al’umma kan daƙile shayin miyagun ƙwayoyi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Dangane da muguwar yawaitar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, Ƙungiyar Matasa ta Ƙasa (NYCN) da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA) na neman haɗin kan al’ummomi da ƙungiyoyi wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya.

Dangane da rahoton ƙwayoyi na duniya na 2021, wanda Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ya fitar, kusan mutane miliyan 275 ne ke amfani da ƙwayoyi a duk duniya, yayin da sama da mutane miliyan 36 ke fama da matsalar shan muggan ƙwayoyi.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa, Nijeriya na da kusan mutane miliyan 14.3 masu shan muggan ƙwayoyi waɗanda kusan miliyan 3 ke fama da matsalar shan muggan ƙwayoyi.

Abubuwan haɗari na amfani da miyagun ƙwayoyi sun fi girma kuma lalacewar masu amfani sun yi ƙamari. Wannan ya sa ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki su binciko dukkan hanyoyin da za su ilimantar da matasa kan illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma a wani yunƙuri na kare lafiyar jama’a.

A wani shiri na ilimantar da matasa, ƙungiyar matasan reshen Legas tare da haɗin gwiwar gidauniyar Imeyreach sun gudanar da wani shiri na wayar da kan matasa mai taken ‘Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta, Lafiya ta’, a unguwar Agege da ke Legas.

Da ya ke jawabi ga matasan, taron da aka yi a kan zaman kwamitin, wani masanin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa daga gidauniyar Imeyreach, Oluwanifesimi Opawale da kuma Kwamandan NDLEA na yankin Agege, Ikeja, Isaac Unuene.

Unuene ya bayyana cewa, haɗin kan al’umma da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a wajen farfaɗo da matasan Nijeriya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya zama dole domin samun nasara baki ɗaya a yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Ya ce, haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci domin hukumar NDLEA ita kaɗai ba za ta iya gudanar da ayyukan da ake buƙata don yanke tushen samar da ƙwayoyi ta hanyar kame masu rarrabawa a cikin al’umma ba.

Mataimakin shugaban ƙungiyar NYCN mai wakiltar Legas ta Yamma, Kwamared Ademosu, Kwamared Jamiu Ademosu ya ce, majalisar za ta cigaba da ƙoƙarinta na kare lafiyar matasa ta hanyar haɗa su waje guda domin samun ilimi kan lafiyar ƙwaƙwalwa da ɗorewa.

Shirin ya samu halartar matasa daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomi 28 na Legas, kuma an amince da wasu zaɓaɓɓun matasa a matsayin jakadu da za su jajirce wajen tabbatar da lafiyar matasa a yankunansu.

A cewar Ademosu, sama da matasa 170 ne suka nemi muƙamin jakadanci, amma bisa tsarin tantancewar, an samu nasarar tantance mutane 25 tare da horar da su kan lafiyar ƙwaƙwalwa da shan muggan ƙwayoyi domin yin aiki a cikin al’umma.

Ya shawarci matasan Nijeriya da su guji duk wani nau’i na miyagun ƙwayoyi da ka iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwarsu wajen gina al’ummar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *