Ƙungiyar matasan Afirka ta faɗakar da matasa illolin tayar da hankali

Daga UMAR AƘILU MAJERI, a Dutse

Ƙungiyar majalisar matasan Afirka reshen jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammad Ado Yusif, ta gudanar da taronta a Jihar Jigawa da nufin faɗakar da matasa muhimmancin zaman lafiya a Nijeriya.

Muhammed Ado ya ce, maƙasudin taron shi ne a faɗakar da matasa illolin tada hankalin al’umma da kuma illar shaye-shaye da matsalolin da rayuwar matasa take a halin yanzu a faɗin Nijeriya.

Ado ya buƙaci matasa su zage dantse wajen neman ilimi, kana su tashi tsaye wajen koyon sana’a domin matasa su ne ƙashin bayan kowacce al’umma.

Shi ma hakimin Chamo, Alhaji Salihi Suleiman wanda shi ne ya wakilci Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhd sunusi a wajen taron, ya yi kira ga matasa da su zama mutane na gari abin koyi.

Ya kuma hori matasan su tsaya a kan gaskiya a duk harkokin rayuwarsu su kuma guji aikata son zuciya, domin muddin matasa suka riƙe gaskiya da amana za a sami sauƙi wajen amfani da matasa a aikata ayyuka marasa kyau a Nijeriya.

A nasa ɓangaren, wakilin kwamashinan ‘yan sandan jihar jigawa, CSP Dahiru Mahamood, ya bayyna cewa zaman lafiya shi ne gaba da komai a cigaban rayuwar al’umma, sai da zaman lafiya ne ake iya kaiwa ga biyan buƙata, don haka ya hori matasa su guji amfani da makamai suna aikata laifin ko tayar da yamutsi.

Mahamood ya ƙara da cewa, matuƙar matasa suka bijire wa dokokin ƙasa, su kuma Jami’an tsaro ba za su bari a riƙa yi wa doka kama karya ba duk wanda ya karya dokar ƙasa za su hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Ya ci gaba da cewa, bazuwar makamai a hannun jama’a ya taimaka wajen samun masu tayar da hankali a Nijeriya saboda haka ne ya zama wajibi jami’an tsaro a Nijeriya su ma su tashi a tsaye wajen yaƙi da bazuwar makamai.